'Tinubu Zai Cire 'Yan Najeriya Miliyan 70 Daga Talauci', Jigon APC, Obidike

'Tinubu Zai Cire 'Yan Najeriya Miliyan 70 Daga Talauci', Jigon APC, Obidike

  • Shugaba Tinubu ya samu yabo ganin yadda ya nada kwararrun ministoci a gwamnatinsa wadanda aka rantsar a yau
  • Honarabul Obidike Chukwuebuka shi ya bayyana haka yayin da sabbin ministoci su ka kama rantsuwar aiki a yau Litinin
  • Ya ce Tinubu zai cire 'yan Najeriya miliyan 70 a kangin talauci ganin irin yadda ya dauko matakan gyara a kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon mamban kwamitin kamfe na shugaban kasa, Obidike Chukwuebuka ya ce Shugaba Tinubu zai tsamo 'yan Najeriya miliyan 70 a talauci.

Honarabul Obidike ya bayyana haka ne yayin da Tinubu ya rantsar da ministoci a yau Litinin 21 ga watan Agusta a Abuja.

Jigon APC ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai cire mutane miliyan 70 daga talauci
Jigon APC Ya Yabi Tsarin Da Shugaba Tinubu Ya Dauko Na Rage Talauci. Hoto: Obidike Chukwuebuka, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Obidike ya ce na shirin Tinubu?

Ya ce rantsar da kwararrun ministocin zai taimaka wurin tsamo 'yan Najeriya daga kangin talauci cikin watanni shida, Vanguard ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira a Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chukwuebuka ya ce cire Najeriya a kangin talauci ba karamin aiki ba ne kuma ya na bukatar jajircewar shugaba.

Amma a bangaren shi ya ce Tinubu ya dauko wannan hanya ganin yadda ya nada kwararrun ministoci a gwamnatinsa.

Obidike ya ce Tinubu ya himmatu wurin inganta hannun jari a harkar noma da taimakon manoma.

Ya bayyana shirin Tinubu a kan noma

Ya kara da cewa ba da karfi a harkar noma zai yi matukar rage kangin talauci ganin yadda 'yan Najeriya su ka dogara da kayan noma don gudanar da rayuwarsu, Newstral ta tattaro.

Ya tabbatar da cewa Tinubu ya himmatu wurin inganta harkokin kasuwanci da kuma ba da tallafi ga kananan 'yan kasuwa don rage talauci.

Ya ce ba da karfi da Tinubu ya yi a harkar ilimi musamman ba da lamuni ga dalibai da kuma tallafin karatu na da matukar tasiri wurin yaye talauci.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Da Bola Tinubu Ya Sauya Wa Ma'aikatu Ana Daf Da Rantsar Da Su

Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Ministoci

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin ministocin da ya nada a kwanakin baya a yau Litinin 21 ga watan Agusta a Abuja.

Daga cikin wadanda su ka samu mukamin ministan akwai Nyesom Wike a matsayin ministan birnin Tarayya, Abuja da kuma Muhammad Badaru Abubakar a matsayin ministan tsaro.

Sauran sun hada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.