'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Dan Sanda Da Matarsa A Jihar Imo
- Wasu ma'aurata sun gamu da ajalinsu a Owerri da ke jihar Imo bayan 'yan bindiga sun bindige su har lahira
- 'Yan bindiga uku ne su ka shammaci Sampson Owobo da mai dakinsa a jiya Lahadi 20 ga watan Agusta
- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Henry Okoye ya tabbatar da faruwar lamarin a Owerri da ke jihar Imo
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Imo - Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani magidanci Mista Sampson Owobo da mai dakinsa a birnin Owerri na jihar.
An kashe Owobo ne wanda tsohon mataimakin Sifetan 'yan sanda ne da matarsa a jiya Lahadi 20 ga watan Agusta.
Meye aka ce kan kisan tsohon dan sandan?
Punch ta tattaro cewa Owobo dan asalin jihar Edo ne kuma kisan nasa ya faru ne kusa da kamfanin sufuri na Chisco a Owerri, Legit.ng ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Vanguard ta tattaro cewa mutane da dama sun shiga damuwa yayin da su ka shige gidajensu da kulle kofofin shiga.
Rahoton ya tabbatar cewa 'yan kasuwa da masu kananan sana'o'i duk sun rufe shagunansu tare da tserewa gidajensu don gudun fitina.
Meye 'yan sanda su ka ce kan kisan?
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Henry Okoye ya tabbatar da faruwar lamarin a Owerri inda ya ce kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin bincike a kan kisan.
Okoye ya ce yanzu haka jami'ansu sun bazama neman 'yan bindigan don hukunta su, cewar Leadership.
Ya ce:
"Kashe wadannan ma'aurata abin takaici ne da kuma abin Allah wadai a wannan yanayi.
"Kwamishinan 'yan sanda a jihar Imo ya yi Allah wadai da wannan kisan gillar inda ya bukaci a yi bincike don kamo wadanda su ka aikata haka."
'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an 'Yan Sanda 2 A Imo
A wani labarin, 'yan bindiga sun yi ajalin jami'an 'yan sanda guda biyu a karamar hukumar Ngor Okpala da ke jihar Imo.
'Yan bindigan da ake zargin 'yan kungiyar Eastern Security Network (ESN) sun kai wa 'yan sandan harin ne a shingen binciken ababan hawa.
Ana zargin kungiyar ESN din da alaka da kungiyar fafutukar yankin Biafra (IPOB) da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng