'Yan Ta'adda Sun Shiga Rudani Tun Bayan Nada Matawalle Minista, Anas Kaura
- Kwamred Anas Kaura, Hadimin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yabi Shugaba Tinubu kan nadin Matawalle
- Kaura ya ce a yanzu haka 'yan ta'adda da sauran masu laifuka sun shiga taitayinsu
- Kwamred Anas ya bayyana haka ne a daren jiya Lahadi 20 ga watan Agusta a Kaduna inda ya ce Matawalle zai sauya fasalin tsaron kasar
Jihar Kaduna - Hadimin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, Abdullahi Anas Kaura ya ce nadin mai gidansa a matsayin minista ya saka 'yan ta'adda cikin mayuyacin hali.
Kwamred Anas Kaura ya bayyana haka a daren jiya Lahadi 20 ga watan Agusta a Kaduna.
Meye Kaura ya ce game da Matawalle?
Anas Kaura ya ba wa 'yan Najeriya tabbacin samun zaman lafiya da kare martabar kasar daga sabon ministan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce nadin Matawalle kalubale ne ga masu kawo cikas a zaman lafiyar kasar, cewar Vanguard.
A cewarsa:
"Nadin Matawalle ya zo a daidai wurin shawo kan rikici tsakanin Fulani da makiyaya.
"Har ila yau, nadin Matawalle ya jefa masu aikata laifuka da kuma son zubar da jini don biyan bukatar kansu cikin mawuyacin hali.
"Zai yi kokari wurin inganta jami'an tsaron kasar da kara inganta diflomasiyya da kuma kiyaye iyakar Najeriya."
Me ya ce game da nadin Matawalle ga Tinubu?
Kaura ya kara da cewa ma'aikatar tsaro a karkashin kulawar Matawalle za ta kawo ci gaba mai dumbin yawa a rundunar tsaron kasar.
Ya ce shi shaida ne a kan yadda Matawalle ya dage wurin yi wa kasa aiki da kuma kare lafiyar al'umma.
Ya ce:
"Matawalle shi ne gwamna na farko da ya kawo tsarin wurin zama na RUGA ga Fulani tare da asibiti da makaranta da kuma kasuwa."
A karshe ya godewa Shugaba Tinubu wurin zakulo kwararru da za su rike masa mukamai a gwamnatinsa, Independent ta tattaro.
Matawalle Ya Bukaci Dauda Lawal Na Zamfara Ya Yi Murabus
A wani labarin, Anas Kaura hadimin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bukaci gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi murabus.
Anas ya fadi haka ne bayan gwamnan ya gagara tabuka komai a harkar tsaron al'ummar jihar.
Ya ce tun bayan hawan Dauda Lawal, ake samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a jihar.
Asali: Legit.ng