Rabaran Mbaka Ya Yi Wani Mummunan Hasashe a Kan Shugaba Tinubu
- An buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi taka tsan-tsan domin kauce jefa ƙasar cikin irin abin da ya faru a Jamhuriyar Nijar
- Fr Ejike Mbaka, shugaban cocin AMEN, ya ce shugaban ƙasar yana buƙatar ya miƙa lamuransa ga Allah domin ceto ƙasar nan
- Babban faston ya ce idan har shugaban ƙasar ya ƙi sauraron abin da ya faɗa, hakan zai janyo mummunan bala'i wanda bai san yaushe ko ta yadda zai zo ba
Jihar Enugu - Rabaran Fr. Ejike Mbaka, shugaban cocin 'Adoration Ministry in Enugu, Nigeria' (AMEN), ya hango wani rikicin siyasa da zai faru a ƙasar nan wanda ya fi na Jamhuriyar Nijar, saboda ƙaruwar rashin aikin yi da a ke fama da shi a ƙasar nan.
A cikin bidiyon da aka sanya a shafin cocin na Youtube, babban faston ya yi gargaɗin cewa ubangiji yana kallon Shugaba Bola Tinubu, sannan shugaban ƙasar zai iya gyara ƙasar nan idan ya miƙa lamuransa ga ubangiji.
Fr Mbaka, a lokacin jawabin na sa ya koka kan halin da ƙasar nan ke ciki, musamman rashin aikin yi, inda ya ƙara da cewa yakamata a yi ƙoƙarin magance matsalar cikin gaggawa.
An yi sabon hasashe a kan Shugaba Tinubu
A cewar malamin addinin, yakamata cikin gaggawa shugaban ƙasar ya koma ga ubangiji ko a samu mummunan sakamako cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Fr Mbaka ya bayyana cewa:
"Ƙaruwar rashin aikin yi a Najeriya ya yi yawa. Ubangiji yana kallon Shugaba Tinubu. Idan ya miƙa lamuransa ga ikon ubangiji, ubangiji zai yi amfani da shi domin ceto Najeriya."
"Idan Shugaba Tinubu ba ya son miƙa lamuransa ga ubangiji, na hango wani mummunan abu fiye da wanda yake faruwa a Nijar zai faru a Najeriya. Ban san ta yaya ba, da lokacin da hakan zai faru, amma ubangiji ya sanar min da hakan."
Mbaka yana ɗaya daga cikin malaman addinin kiristoci da su ke hango faruwar abubuwa a Najeriya.
Ayodele Ya Gargadi Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, shugaban cocin Evangelical Spiritual Church, Primate Ayodele, ya aike da sabon saƙo zuwa ga Shugaba Bola Tinubu.
Ayodele ya gargaɗi shugaban ƙasar kan halin ƙuncin da ake ciki a Najeriya, inda ya ce idan ba a kula ba, ƴan Najeriya na iya yin bore a ƙasa.
Asali: Legit.ng