Tinubu Ya Nada Sabon Minista, Ya Canjawa Wasu Ministoci Ma’aikatu
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon ministan ci gaban Niger Delta a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta
- Injiniya Abubakar Momoh ya zama sabon ministan ci gaban Niger Delta
- Haka kuma, Shugaban kasar ya sauyawa wasu ministocinsa ma'aikatu kuma ya ce umurnin ya fara aiki nan take
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Injiniya Abubakar Momoh a matsayin ministan ci gaban Niger Delta, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa wanda kakakinsa, Ajuri Ngalale, ya saki a madadinsa a daren ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.
Da farko Tinubu ya tura Momoh ma’aikatar matasa ne.
A cikin sanarwar, shugaban kasar ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a nada sabon ministan matasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tinubu ya sauyawa wasu ministocinsa aiki
Shugaban kasar ya kuma sauya wa wasu zababbun ministocinsa ma’aikatu kamar haka:
"(A) An canjawa H.E. Adegboyega Oyetola wuri a matsayin ministan tattalin arzikin teku
(B) An canjawa Hon. Bunmi Tunji-Ojo wuri a matsayin ministan harkokin cikin gida.
"(C) An sauyawa Sa’idu Alkali wuri a matsayin ministan sufuri
“Bugu da kari, yanzu kananan ministoci biyu a bangaren Man Fetur da Gas sun samu matsuguni a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya kuma sune kamar haka:
“(i)Sen. Heineken Lokpobiri shine karamain ministan mai (Oil), ma'aikatar albarkatu man fetur.
“(ii) Hon. Ekperipe Ekpo shine karamar ministar Gas, ma'aikatar albarkatun man fetur.
Shugaban kasar ya kuma amince da sauya sunan ma'aikatar muhalli da kula da muhalli ta tarayya zuwa ma'aikatar muhalli ta tarayya
Sanarwar ta kara da cewa:
"Duk sauye-sauyen da aka ambata za su yi aiki nan take da wadannan umarnin shugaban kasa."
Kungiyar SERAP ta aika gagarumin sako ga Tinubu kan Wike da sauransu
A wani labarin, mun ji cewa kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da Ma'aikatun gwamnati (SERAP), ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni daga karbar kudin fansho daga jihohinsu.
Kungiyar mai zaman kanta ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng