Injiniyoyi Mata Sun Shawarci Tinubu Ya Ba Su Damar Gyara Matatun Man Najeriya Baki Daya

Injiniyoyi Mata Sun Shawarci Tinubu Ya Ba Su Damar Gyara Matatun Man Najeriya Baki Daya

  • Kungiyar kwararrun mata injiniyoyi ta Najeriya (APWEN) ta shaida wa shugaba Tinubu cewa injiniyoyi mata za su iya farkar da matatun man Najeriya da suke bacci a cikin shekara guda
  • Yayin wani lacca da aka gudanar a Legas, shugabar kungiyar ta APWEN, Atinuke Owolabi, ta ce injiniyoyi mata a shirye suke su hada kai wajen gyara matatun man
  • Owolabi ta kuma jaddada mahimmancin karfafawa injiniyoyin cikin gida da kuma rage dogaro ga kwararrun ‘yan kasashen waje

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos, Nigeria - Kungiyar kwararrun mata injiniyoyi ta Najeriya (APWEN) ta shaida wa shugaban kasa Bola Tinubu cewa injiniyoyi mata za su iya gyara matatun man kasar nan da suka lalace cikin shekara guda.

Shugabar kungiyar ta APWEN, Atinuke Owolabi, ta bayyana haka ne a yayin taron lacca da taron shekara-shekara na kungiyar a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta a Legas.

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

Ta ce injiniyoyi mata a Najeriya suna da karfin farkar da matatun mai da ke barci a cikin shekara guda, inji rahoton TheCable.

Injiniyoyi mata na neman Tinubu ya ba su dama
Bola Tinubu, shugaban kasar Najeriya | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewarta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dukkanin injiniyoyi mata a shirye suke su taru domin ganin yadda za mu samar da mafita, tare da tabbatar da cewa mun gyara wadannan matatun man.
“Don haka muna kira ga shugaban kasar mu da ya kalubalanci mata injiniyoyi su gyara wadannan matatun man, kuma ina so in tabbatar maku cewa, a cikin shekara guda, za mu tabbatar da cewa an fara aiki da matatun da yardar Allah.”

Ya kamata dama da injiniyoyin ’yan kasa

Owolabi ta kara jaddada bukatar karfafa injiniyoyin cikin gida Najeriya, inda ta ce Najeriya na bukatar rage dogaro ga kwararrun ‘yan kasashen waje, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ta roki shugaba Tinubu da gwamnonin jihohi su kara ba injiniyoyin cikin gida damar yin ayyuka masu ma’ana a kasar nan.

Kara karanta wannan

Da walakin: Tinubu zai iya bin tafarkin Buhari wajen rike kujarar minista mai tsoka

A kalamanta:

"Ina kuma rokon shugabanninmu, musamman shugaban kasa da gwamnoninmu, da su karfafa injiniyoyi ‘yan asalin kasar nan saboda muna da kwarewa."

Dan Najeriya ya zama kwarzon injiniya

A wani labarin, kamar yadda WFEO ta bayyana a shafinta na Twitter, Mustafa Balarabe Shehu FNSE FAEng ya lashe zaben sabon WFEO da aka yi a makon nan.

Sanarwar da aka fitar a Twitter a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris 2022 da kimanin karfe 1:00 na dare ya tabbatar da nasarar ‘Dan Najeriya a wannan zabe.

Kungiyar Injiniyoyi da masu zayyana na reshen kasar Kosta Rika su ka gudanar da wannan zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.