Labari mai dadi: Yadda injiniyoyi 2,000 za su samu aiki a matatar man Dangote

Labari mai dadi: Yadda injiniyoyi 2,000 za su samu aiki a matatar man Dangote

- Akalla injiniyoyi 2,000 ne ake sa ran za su samu gurbin aiki a matatar man Dangote da zaran ta soma aiki, lamarin da zai kawo raguwar rashin ayyuka a kasar

- Babban daraktan kamfanin Dangote, Mr Edwin, ya ce akwai katafaren bangaren sarrafa tyaki da sinadaran da ake samunsu daga man fetur a cikin matatar

- Anyi amfani da kayayyakin fasahar zamani a matatar man ta Dangote da za ta iya gogayya da duk wata matatar mai da ke a kasashen turai

Kafuwar matatar man fetur ta Dangote da kuma soma aikinta zai taimaka matuka gaya wajen kawo karshen matsalolin rashin aikinyi da kasar ke fama da su, kasancewar za a dauki akalla injiniyoyi 2,000 aiki domin gudanar da ayyukansu na yau da kullum a matatar.

Babban daraktan kamfanin Dangote a fannin tsare tsrae da bunkasa ayyukan masana'antu, Mr Devakumar Edwin, ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakunci wata tawagar shuwagabannin asusun tallafi na man fetur (PTDF) a ziyarar da suka kaiwa babban ofishin kamfanin Dangote da ke Legas.

A cewar sa, akwai dubunnan guraben ayyuka ga jama'a musamman ganin cewa akwai katafaren bangaren sarrafa tyaki da sinadaran da ake samunsu daga man fetur a cikin matatar.

KARANTA WANNAN: Mulki da kudi: Saraki ya taya Aliko Dangote murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Labari mai dadi: Yadda injiniyoyi 2,000 za su samu aiki a matatar man Dangote
Labari mai dadi: Yadda injiniyoyi 2,000 za su samu aiki a matatar man Dangote
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ganga 650,000 a kowacce rana da matatar man Dangote za ta rinka samarwa na kan gaba cikin tsari, kuma matatar ce kwallin kwal mafi girma da kaso 50 a fadin duniyar; kuma anyi amfani da kayayyakin fasahar zamani da zasu iya gogayya da suk wata matatar mai a kasashen turai.

Mr Edwin, wanda kuma ya bayyana cewa kwarewar ma'aikata a har kullum shi ne babban jarin ko wanne kamfani da ya samu nasara, ya bayyana hakan a zantawarsa da shuwagabannin PTDF, a ziyarar da suka kai babban ofishin kamfanin Dangote da ke Legas.

Da ya ke yi masu karin bayani kan matatar man Dangote, babban daraktan ya kuma ce, "duk da cewa mafi akasarin matatun man fetur a kasashen waje sun mayar da hankali wajen sarrafa sinadarin man 'diesel', amma matatar man Dangote za ta mayar da hankali wajen sarrafa sinadarin iskar gas fiye da 'diesel', sinadarin da muka fi amfani da shi a nan."

Dangane da ayyukan matatar kuwa, Edwin ya bayyana cewa, "mun tsara daukar ma'aikata bisa tsari na kasashen turai da Amurka. Dangane da ma'aikata kuwa, muyn samu bukatar neman aiki daga dubunnan 'yan Nigeria, kuma muna bin matakan da suka dace domin tantancewa tare da turasu kasar India da sauran kasashe domin samun horo na musamman."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel