Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Dan Siyasa Da Wasu 2 a Kaduna
- Wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kansila a anguwar Mai Taro da ke karamar hukumar Sabo ta jihar Kaduna
- Maharan sun kuma sace wata mata tare da kansilan sannan suka kuma yi awon gaba da wani a unguwar Dankande
- Sai dai zuwa yanzu rundunar yan sanda ko gwamnatin jihar bata tabbatar da harin da aka kai a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, ba a hukumance
Jihar Kaduna - Tsagerun yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun yi awon gaba da kansilan gudunmar Garu da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna, Alhaji Sabitu Ahmad, da wasu mutane biyu.
An tattaro cewa maharan sun farmaki yankin Anguwar Mai Taro inda kansilan yake da zama sannan suka yi awon gaba da shi tare da wata mata a unguwar a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta.
Yan Sanda Sun Kama Karin Mutum 3 Cikin Wadanda Suka Yi Wa Sarkin Kano Ihun ‘Sabon Gwamna Sabon Sarki’
Yan bindiga sun sace kakakin kansilolin karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna
Jaridar Aminiya ta rahoto cewa, an kuma sace wani mutum guda a Unguwar Dankande da ke karamar hukumar ta Soba a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin yankin mai suna Lawal Sani ya sanar da jaridar Aminiya cewa Kansilan da aka sace shine mai magana da yawun kansiloli a yankin.
Martanin rundunar yan sanda
Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ba domin baya amsa wayarsa kuma bai amsa sakon da aka tura masa ba.
Sai dai kuma, mai magana da yawun Gwamnar Jihar, Mohammmed Lawan Shehu ya ce har yanzu ba a sanar da shi lamarin ba a hukumance.
Yan bindiga sun sace fasto, sun kashe matarsa a jihar Edo
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe Misis Peace Chinyereugo, matar faston cocin Vineyard of Grace Dominion Assembly, Rev. Samuel Chinyereugo, a garin Benin, babban birnin jihar Edo.
Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:36 na yammacin ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, a harabar cocin da ke lamba ta 101, Unguwar Upper Lawani, New Benin, garin Benin.
Asali: Legit.ng