Gwamnan Jihar Neja Ya Nada Mata 131 Sabbin Mukamai a Jihar
- Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya nuna zai dama da mata a gwamnatinsa domin ciyar da jihar gaba
- Gwamna Bago ya naɗa mata 131 a sabbin muƙamai daban-daban a jihar domin bayar da ta su gudunmawar wajen ciyar da jihar gaba
- Naɗin da gwamnan ya yi wa matan na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe na ba mata dama a gwamnatinsa
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya amince da naɗin sabbin muƙamai a jihar.
Gwamna Bago a cikin sabon naɗin muƙaman da ya yi, ya nada mata 131 a kan muƙaman siyasa daban-daban a jihar, cewar rahoton Daily Trust.
Kakakin gwamnan jihar, Bologi Ibrahim, a cikin wata sanarwa ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, ya tabbatar da sabbin naɗe-naɗen da gwamnan ya yi.
Bologi ya bayyana cewa an naɗa mata 41 a matsayin kodinetoci ne, yayin da sauran 90 ɗin aka naɗa su a matsayin masu taimakawa na musamman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da yake taya su murnar naɗin da aka yi musu, gwamnan ya buƙace su da su jajirce wajen bayar da ta su gudunmawar domin samun nasarar gwamnatinsa.
Dalilin Bago na naɗa mata 131
Bago ya bayyana cewa naɗin da ya yi musu na daga cikin cika alƙawarin da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, na ba mata dama su bayar da gudunmawarsu wajen cigaban jihar.
Ya bayyana cewa an zaɓo su ne bisa cancantarsu, dattako da ƙwarewar da suka samu a wuraren da suka yi aiki a baya, rahoton The Cable ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa matan da aka naɗa za su taka rawar gani wajen haɓɓaka shirin gwamnatinsa na ƙara inganta rayuwar mutanen jihar.
Tun da farko gwamnan ya yi alƙawarin zai gwangwaje mata da muƙamai 100 a gwamnatinsa.
Filin Jirgin Saman Minna Na Dab Da Fara Aiki
A wani labarin kuma, filin tashi da sauka na jiragen sama da ke a birnin Minna na jijar Neja, na dab da fara aiki.
Gwamnan jihar Mohammed Umaru Bago shi ne ya bayar da wannan tabbacin, inda ya ce tuni har ya fara tattaunawa da kamfanunnikan jiragen sama domin fara jigila a filin jirgin.
Asali: Legit.ng