Yan Nijar Sun Yi Zanga-Zangan Goyon Bayan Bazoum A Kano
- 'Yan Nijar mazauna jihar Kano sun yi zanga-zanga don nuna goyon baya ga gwamnatin Bazoum
- Matasan da ke zanga-zangan sun kuma nuna goyon bayansu ga kungiyar ECOWAS
- Sun roki ECOWAS da su yi duk mai yiyuwa don mayar da mulki ga hambararren shugaban
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Daruruwan 'yan Nijar da ke zaune a jihar Kano sun gudanar da zanga-zangan lumana don goyon bayan Mohamed Bazoum.
Mutanen na zanga-zangan ne don neman a dawo da hambararren shugaban kasar, Bazoum kan mulki.
Meye dalilin yin zanga-zangan a Kano?
Idan ba a mantaba a ranar 26 ga watan Yuli ne sojoji su ka kifar da gwamnatin Bazoum kan wasu korafe-korafe a kansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta umarci dakarunta su tsaya cikin shiri don afkawa Nijar idan ba su mika mulkin ba.
Amma 'yan Nijar da ke jihar Kano a safiyar yau Asabar 19 ga watan Agusta sun cika titunan birnin su na bukatar a dawo da Bazoum kan mulki.
Masu zanga-zangar sun cika shatatalen Triumph da ke karamar hukumar Fagge a cikin Kano don nuna goyon baya ga Bazoum, Daily Nigerian ta tattaro.
Su na dauke da kwalaye da ke dauke da sakwanni da dama don nuna damuwarsu kan mulkin sojin kasar.
Meye masu zanga-zangan a Kano su ke so?
Daga cikin sakwannin da su ke dauke da su akwai "Mu na goyon bayan ECOWAS" da "Ba ma son juyin mulki" da "Ba ma bukatar kama karya" da sauransu.
Shugaban masu zanga-zangan, Lawwalli Barmo ya ce sun fito ne don nuna damuwa kan irin halin da kasar Nijar ke ciki a siyasance.
Ya ce sun yi zanga-zangan ne don nuna goyon bayansu ga zababben shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, cewar Vanguard.
Ya ce:
"Ba mu ga dalilin yin juyin mulki ba, an yi ne don kawo rudani a kasar mu da aka santa da zaman lafiya.
"Don haka muna kira ga sojojin juyin mulki da zu mayar wa Bazoum mulkinsa.
"Mu na kira ga kungiyar ECOWAS da su bi duk wata hanya don dawo da mulki ga Bazoum."
ECOWAS Ta Fadi Ranar Da Za Ta Afkawa Nijar
A wani labarin, Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) sun ce dakarunsu a shirye su ke kawai umarni su ke jira don afkawa kasar Nijar.
Wannan na zuwa ne bayan ECOWAS ta ba wa sojojin damar mika mulki ga Mohamed Bazoum da su ka hambarar a watan Yuli.
Asali: Legit.ng