Abubakar Momoh: Tsohon Malamin Sakandare, Tsohon Shugaban SUG, Da Wasu Abubuwa Kan Sabon Ministan Matasa

Abubakar Momoh: Tsohon Malamin Sakandare, Tsohon Shugaban SUG, Da Wasu Abubuwa Kan Sabon Ministan Matasa

FCT, Abuja - An samu sabon minista a ma'aikatar Matasa ta Tarayya, wanda zai jagoranci ma'aikatar shi ne Abubakar Momoh

Bayan kasancewar shi kwararren Injiniya akwai wasu abubuwa muhimmai da ya kamata ku sani game da Momoh.

Abubuwa 10 da ba ku sani ba game da sabon ministan matasa, Abubakar Momoh
Abubakar Momoh Na Daga Cikin Sabbin Ministoci Da Za A Rantsar. Hoto: JesusSon Lucky Apeakhuye-Agbukor.
Asali: Facebook

Yayin da ake shirin rantsar da ministoci a ranar Litinin 21 ga watan Agusta, akwai abubuwa 10 da baku sani ba game da Momoh.

1. Tsohon dan majalisar Wakilai

Momoh ya wakilci mazabar Etsako a jihar Edo har wa'adi biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kasance mamban jam'iyyar APC kafin sauya sheka zuwa PDP inda ya tsaya takarar Sanata ya fadi.

Daga bisani ya dawo jam'iyyar APC bayan shan kaye da ya yi, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

2. An haifi Momoh a Etsako

An haifi Momoh a karamar hukumar Etsako ta Gabas da ke jihar Edo.

Etsako na daga cikin manyan kabilu uku da ke jihar.

3. Tsohon makamin sakandare

Momoh ya taba koyarwa a makarantar Ekperi Grammar kafin samun digiri a jami'ar Benin.

Momoh na matukar sha'awar harkar ilimi a rayuwarsa.

4. Tsohon shugaban dalibai

A lokacin da ya ke jami'ar Benin, Momoh ya tsunduma harkar siyasar dalibai wanda hakan ya ba shi damar kasancewa shugaban daliban jami'ar.

5. Tsohon kansila

Momoh ya taba rike mukamin kansila a yankinsa na karamar hukumar Etsako lokacin dawowar dimokradiyya.

6. Dan siyasa

Vanguard ta bayyana Momoh a matsayin dan siyasa tun daga tushe.

Momoh ya yi imanin cewa mafi kyawun siyasa ita ce tun daga tushe.

7. Ilimi

Momoh ya ci gaba da karatu bayan digiri na farko.

Ya yi digiri na biyu a jami'ar Legas, sannan ya kasance mamban kungiyar injiniyoyin Najeriya da sauran kungiyoyi.

Kara karanta wannan

Jerin Ministoci 5 Da Tinubu Ya Daura Wa Alhakin Kawo Karshen Rashin Tsaro A Najeriya

8. Mai biyayya ga Oshiomhole

Momoh ya kasance mai biyayya matuka ga tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

Momoh na daga cikin wadanda su ka yi ruwa da tsaki na tabbatar da Oshiomhole ya zama gwamna a 2017 karkashin jam'iyyar AC.

9. Zargin cewa Oshiomhole ne ya tura sunansa

Mutane na ta yada cewa Oshiomhole ne ya tura sunan Momoh ga Shugaba Tinubu don ba shi mukamin minista.

10. Ya na rike da sarautar gargajiya da dama

Momoh na rike da sarautar gargajiya a jihar Edo kamar su Otsegbhe na Okpella da Ezomo na Ibie.

Har ila yau, shi ne Udi na Auchi da Obhada na Okpe da kuma Okhai na Ibie ta Kudu.

Tinubu Zai Rantsar Da Sabbin Ministoci A Ranar Litinin

A wani labarin, Shugaba Tinubu zai rantsar da sabbin ministoci 45 a ranar Litinin 21 ga watan Agusta.

Za a rantsar da ministocin ne bayan kammala tantance su da majalisar Dattawa ta yi a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.