Badakalar N6.9bn: Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Ta Hannun Daman Emefiele

Badakalar N6.9bn: Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Ta Hannun Daman Emefiele

  • Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi fatali da ƙarar da ma'aikaciyar CBN, Sa'adatu Yaro ta shigar akan DSS
  • Sa'adatu Yaro ta buƙaci kotun da ta bayar da umarnin a hukumar ta sakar mata motocinta sannan a bayar da belinta
  • Ma'aikaciyar ta CBN tana cikin waɗanda ake ƙara tare da dakataccen gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele kan badalaƙalar N6.9bn

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta yi fatali da ƙarar kare haƙƙi da ma'aikaciyar babban bankin Najeriya (CBN), Sa'adatu Yaro, ta shigar akan hukumar ƴan sandan farin kaya ta ƙasa (DSS).

Jaridar The Punch ta rahoto cewa kotun ta yi fatali da ƙarar ne a ranar Juma'a, 18 ga watan Agustan 2023.

Kotu ta yi fatali da karar ta hannun daman Emefiele
Kotu ta kori karar da ta hannun daman Emefiele ta shigar da DSS Hoto: @timmybello
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Yaro, a cikin karar tana neman kotun ta bayar da umarnin a sakar mata tsala-tsalan motocinta guda shida da hukumar ta ƙwace.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Ba Alkalai Cin Hancin N10m, Ta Bayar Da Dalilai

Ta kuma buƙaci kotun da ta bayar da umarnin a bayar da belinta kan cigaba da tsareta da hukumar ke yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa yakamata DSS su sake ni - Sa'adatu Yaro

Yaro ta hannun lauyanta ta bayyana cewa cigaba da tsareta da azabtar da ita da hukumar DSS ke yi tun ranar 12 ga watan Yuli, ya saɓawa ƴancin da take da shi na darajar ɗan Adam kamar yadda yake ƙunshe a cikin sashi na 34 da 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Babbar ma'aikaciyar ta CBN tana cikin waɗanda gwamnatin tarayya ke ƙara akan baɗakalar N6.9bn, da ake tuhumar dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Gwamnatin tarayya dai ta gurfanar da Godwin Emefiele tare da Sa'adatu Yaro bisa zargin karkatar da makuɗan kuɗi har N6.9bn.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Matashi Gaban Kuliya Bisa Zargin Tafka Ta'asa a Makabarta a Legas

Jsmi'an DSS Sun Cafke Shugaban NIRSAL

A wani labarin kuma, kun ji cewa binciken dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya ya sanya an cafke shugaban hukumar NIRSAL.

Abbas Umar Masanawa ya shiga hannun DSS ne bayan bincike ya iso kansa kan abubuwan da suka riƙa faruwa a bankin CBN a ƙarƙashin Godwin Emefiele.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng