Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Kan Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Kan Sojojin Juyin Mulkin Nijar

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi sojojin juyin mulkin Nijar kan lafiyar Shugaba Bazoum
  • Shugaba Tinubu ya gargaɗi sojojin cewa za su kuka da kansu idan rashin lafiyar hamɓararren shugaban ƙasar ta taɓarɓare a hannunsu
  • A halin da ake ciki, ƙungiyar WFU ta nemi a saukaka takunkumin shigo da abincin ayyukan jinƙai a Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gargaɗi ga sojojin juyin mulkin Nijar dangane da lafiyar hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum.

Shugaba Tinubu ya yi gargaɗin cewa akwai hukunci mai tsauri idan sojojin suka bari lafiyar Shugaba Bazoum ta taɓarɓare a dalilin cigaba da tsare shin da su ke yi, cewar rahoton Daily Trust.

Shugaba Tinubu ya gargadi sojojin juyin mulkin Nijar
Shugaba Tinubu ya gargadi sojojin kan lafiyar Bazoum Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bazoum, tare da iyalansa na cigaba da kasancewa a tsare a gidansa tun bayan da sojojin suka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Kara karanta wannan

Abinda Sakataren Amurka Ya Faɗawa Tinubu Kan ECOWAS Dangane Da Juyin Mulkin Nijar

Wani jami'in ƙungiyar tarayyar Turai (EU), Charles Michel, shi ne ya bayyana hakan bayan tattaunawa da Shugaba Tinubu ta wayar tarho a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta rahoto cewa a lokacin tattaunawar jami'in EU ɗin da Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS mai adawa da juyin mulkin Nijar, ya bayyana cewa lafiyar Shugaba Bazoum ƙara taɓarɓarewa take yi.

Akwai yunwa a Nijar

A halin da ake ciki, ƙungiyar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya (WFP), ta yi gargaɗin cewa rikicin na Nijar zai haifar da yunwa a ƙasar mai fama da talauci.

Kulle iyakar da ke tsakanin Nijar da Benin ta sanya an dakatar da shigo da abinci ta hanyar tashar jirgin ruwan da ke birnin Cotonou.

WFP a Nijar tana buƙatar a bari a riƙa shigo da abinci domin aikin jinƙai sabids kaucewa aukuwar wani sabon bala'i.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Nijar Za Su Tuhumi Shugaba Bazoum, Sun Bayyana Dalilai

UN ta bayyana cewa tun kafin a yi juyin mulkin, sama da mutum miliyan uku na ƙasar na fama da matsalar rashin abinci.

Dakarun ECOWAS Sun Shirya Kai Hari a Nijar

A wani labarin kuma, dakarun sojojin ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) sun shirya kai farmaki a Jamhuriyar Nijar.

Sojojin sun bayyana cewa sun shirya tsaf domin kawar da sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Bazoum, ta hanyar amfani da ƙarfin soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng