Yan Bindiga Sun Sace Matar Wani Faston RCCG a Jihar Kwara

Yan Bindiga Sun Sace Matar Wani Faston RCCG a Jihar Kwara

  • Mrs Blessing Ajiboye ta faɗa hannun ƴan bindiga.bayan sun kawo mata farmaki tana tsaka kasuwanci a shagonta
  • Blessing Ajiboye wacce matar fasto Johnson Olalekan Ajiboye ce, ta shiga hannun ƴan bindigan ne a ƙauyen Elerinjare na jihar Kwara
  • Ƴan bindigan sun yi awon gaba ɗa matar ne bayan sun sauke jaririn da ke goye a bayanta inda suka ajiye shi a ƙasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kwara - Ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun sace matar wani faston cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) a jihar Kwara.

Ƴan bindigan waɗanda sun kai su mutum bakwai, sun sace matar faston ne a ƙauyen Elerinjare da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar, cewar rahoton Channels tv.

Yan bindiga sun sace matar fasto a jihar Kwara
Yan bindigan sun sace matar faston ne a shagonta Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Matar faston mai suna Mrs Blessing Ajiboye, an sace ta ne tare da masu taimaka mata su biyu a shagonta.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummuna Hari Wata Jiha Kan Wani Sanannen Malamin Addini, Sun Halaka Matarsa

Sai dai, daga baya an sako masu taimaka mata a shagon bayan an yi awon gaba da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya auku

Bincike ya nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:45 na daren ranar Alhamis, a shagon wanda faston da matarsa su ke zama.

Da yake bayyana yadda lamarin ya auku, fasto Johnson Olalekan Ajiboye, ya bayyana cewa biyu daga cikin ƴan bindigan da suka kawo farmakin mata ne, sannan sun kawo farmakin ne ta cikin dajin da ke bayan makarantar firamaren ƙauyen.

Fasto Ajiboye, ya bayyana cewa ya fita daga shagon domin ɗauko wani abu ne gida lokacin da ya jiyo ƙarar harbe-harben bindiga.

"Ƴan bindigan ba su ɗauki komai ba a shagon. Kawai sun sace matata mai shekara 34 a duniya, Blessing Ajiboye, bayan sun sauke jaririn da ke goye a bayanta. Sun aje jaririn ne a ƙasa." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Wata Jiha Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Ma'aurata

An kuma tattaro cewa harsashi ya samu wani makwabcin su da ke zaune kusa da shagon, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya bayyana cewa har yanzu bai samu cikakkun bayanai ba kan abin da ya faru.

Yan Bindiga Sun Sace Wasu Ma'aurata

A wani labarin kuma,.wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aurata a jihar Ebonyi da ke yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

Ƴan bindigan sun dai tare ma'auratan ne akan hanya yayin da su ke ƙoƙarin koma zuwa gida bayan sun je unguwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng