ISWAP Ta Kalubalanci Yan Boko Haram Don Fafatawa A Dajin Sambisa
- Kungiyar ta'addanci na ISWAP ta gayyaci takwararta na Boko Haram zuwa filin daga domin su yi musayar wuta
- Kamar yadda ISWAP ta rubuta a wasikar da ta aikewa kungiyar ta'addancin, za su fafata ne a dajin Sambisa ta jihar Borno
- Tuni Boko Haram ta amsa tayin inda suka yi ba ta kashi, an kuma kashe mayaka da dama daga kungiyoyin biyu
Jihar Borno - Kwararren masanin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ya ce ya samu wata wasika daga kungiyar ISWAP zuwa ga Boko Haram na Abubakar Shekau, tana mai kalubalantarta don su zo su fafata.
Zagazola ya yi ikirarin cewa ISWAP ta zargi kungiyar Boko Haram da batar da mutane, suna yada karya, suna boye gaskiya, aikata rashawa da kuma yi wa mata gyade da sunan bautawa Allah.
Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe
Boko Haram ta amsa gayyatar, sun yi musayar wuta
Hakan na kunshe ne a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta, inda ya bayyana cewa tuni bangaren Boko Haram suka amshi tayin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, an yi fafatawan ne a Gaizuwa, inda aka kashe mayaka da dama daga bangarorin guda biyu.
Boko Haram ta kama mayakan ISWAP 60
Ku tuna cewa kwararren masanin tsaron ya wallafa jawabai da dama a ranar Laraba yana ikirarin cewa mayakan Boko Haram sun kama yan ta'addan ISWAP 60 ciki harda manyan kwamandojinsu guda uku.
Ya kuma bayyana cewa an kama yan ta'addan na ISWAP a hanyarsu ta zuwa Damasak a jihar Borno, yana mai bayyana kwamandojin a matsayin Abubakar Saddiq, Abou Maimuna da Malam Idris.
Shari'ar Gwamnan Kano: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Roki Yan Najeriya Su Taya APC Addu'ar Samun Nasara Kan PDP
Ya rubuta:
"Rahoto na musamman: ISWAP ta gayyaci Boko Haram don fafatawa a dajin Sambisa.
"Zagazola ya samu wasika na musamman da kungiyar ISWAP ta rubuta zuwa ga bangaren Boko Haram na Abubakar SHEKAU, suna masu kalubalantarsu zuwa yaki.
"A wasikar zuwa Boko Haram, ISWAP ta ce: 'Mun gargade ku game da abun da kuke yi, daga kashe-kashe, lalata kayayyakin mutane, da cin zarafi a Jihadinmu.
"Sun kuma zargi kungiyar Boko Haram da batar da mutane, yada karya, boye gaskiya, rashawa da yi wa mata fyade da sunan bautar Allah.
"Ku sani, ku sani, ku shirya, za mu bi ku kan batar da mutanenmu. kuma harin zai kasance a wannan rana: “57/Rabi Al-Awwal/9448 AH wanda ya yi daidai da 94/Agusta/5252 AD.
"Tuni Boko Haram ta karbi kalubalen. An yi fafatawar a Gaizuwa inda aka kashe mutane da dama daga bangarorin biyu.
"Kungiyoyin biyu na shirin fafatawa na gaba. Ba a sanar da lokaci da wuri ba."
Boko Haram Ta Cafke 'Yan Kungiyar ISWAP 57 Da Kwamandojinsu 3 A Matsayin Fursunonin Yaki, Ta Bayyana Matakin Gaba
Kwamandan Boko Haram ya mika wuya
A wani labari na daban, mun ji cewa Kwamandan Boko Haram da ya haddasa rikicin ƙabilanci tsakanin 'yan ta'adda wanda ya kai ga kashe mayaka 82 ya mika wuya ga sojoji.
An bayyana cewa kwamandan mai suna Amir Bukkwaram, ya miƙa wuya tare da iyalansa, mayaƙan da ke tare da shi, tarin dabbobi da kuma makamai ga sojoji.
Asali: Legit.ng