Bola Tinubu Ya Soke Tsarin da Gwamnatin Buhari Ta Kawo a CBN Bayan Watanni 25

Bola Tinubu Ya Soke Tsarin da Gwamnatin Buhari Ta Kawo a CBN Bayan Watanni 25

  • Babban bankin Najeriya da aka fi sani da CBN zai cigaba da saida kudin kasar waje ga ‘yan canji
  • Sanarwar ta fito makonni bayan an yi ram da Godwin Emefiele, ana gudanar da bincike a kan shi
  • A watan Yulin 2021, CBN ya daina saidawa ‘yan canji Daloli da sauran kudin ketare a kasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN, ya kawo wasu jerin sababbin matakai da za a rika bi domin saida kudin kasar waje ga ‘yan canji.

Duk wani mai harkar canji watau Bureau De Change (BDCs) a kasar nan, The Cable ta ce sai ya cika sharudan nan kafin ya iya a fadin kasar.

Watanni 25 da su ka wuce, bankin CBN ta sanar da dakatar da saidawa ‘yan canji kudin kasar waje, a lokacin Godwin Emefiele ya na ofis.

Kara karanta wannan

An Samu Satar Mai Sau 114 A Mako Yayin Da Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 46

Shugabannin CBN
Shugabannin bankin CBN Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ka'idoji da sharudan CBN

Daga cikin sharudan da ‘yan kasuwan za su ci karo da su, akwai wajabta masu saida kudin kasashen wajen a kan ribar -2.5% zuwa 2.5%.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bai hallata masu canji su saida kudin kasashen ketaren har ta kai sun ci ribar fiye da 25% ko asarar hakan a kan farashin da su ka canji kudin.

Babban bankin na Najeriya ya yi wannan bayani a shafinsa na yanar gizo a yammacin Juma’a.

Ko a lokacin da aka kawo tsarin da ake amfani da shi kafin yanzu, bankin kasar ya sanar da haka a shafinsa, kusan shekaru biyu kenan a yau.

Daga yanzu dole ne ‘yan canji su rika aikawa da bayanin cinikin da su ka yi a duk rana, kowane mako, wata, watanni hudu zuwa duk shekara.

Tsarin canjin Dala ya fara aiki

Kara karanta wannan

Komai Ya Lafa, Majalisa Ta Fadi Inda Aka Samo Miliyoyin ‘Hutun’ da Aka Biya Sanatoci

Sanarwar ta ce daga lokacin da jawabin nan ya fito, sabon tsarin da aka fito da shi zai soma aiki yayin da ake kokarin tsare darajar Naira a kasar.

Idan kuwa aka samu ‘dan canji bai bayyanawa hukuma cinikin da ya yi ba, wannan zai jefa shi cikin matsalar da za ta shafi sana’ar da yake yi.

Tun daga ukuba mai tsanani, babban bankin kasar ya ce za a iya karbe lasisin aikin duk ‘dan canjin da yake boye gaskiyar cinikin da yake samu.

Ana kuka da tsarin tattakin arziki

Wasu 'yan Najeriya da ke karatu a kasar waje sun shiga uku saboda tashin Dala a kasuwa, yanzu ana maganar kowace Dalar Amurka ta kai N800.

Kun ji labari kungiyar “TETFund Scholars Association in Indiya” ta ce akwai wadanda ke zaune a wajen makaranta da za a kore su saboda kudin haya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng