Tsofaffin Yan Boko Haram Sun Yi Zanga-Zanga Kan Rashin Biyansu Allawus N30,000 a Borno, Sun Tare Hanya

Tsofaffin Yan Boko Haram Sun Yi Zanga-Zanga Kan Rashin Biyansu Allawus N30,000 a Borno, Sun Tare Hanya

  • Tubabbun mayakan Boko Haram sun haddasa cinkoson ababen hawa a babban titin Bulumkutu - Maiduguri
  • Tsofaffin yan ta'addan sun gudanar da zanga-zanga bisa neman a biya su ₦30,000 kamar yadda gwamnati ta yi alkawari
  • Gwamnatin Borno, a kokarin mayar da tubabbun cikin mutanen gari ta cigaba da aikin tantance su bayan faruwar lamarin

Daruruwan mayakan Boko Haram da ke killace a sansanin alhazan Jihar Borno bayan da bayyana tubansu sun gudanar da zanga zanga ranar Juma'a kan neman a biyasu dubu 30 da gwamnati ta yi alkawari.

Tsofaffin mayakan sun kashe titin Bulumkutu zuwa Maiduguri, lamarin da ya janyo cinkoso da hayaniya a yankin, rahoton Zagazola.

Tubabbun Yan Boko Haram Sunyi Zanga-Zanga Kan N30,000 a Borno
Tubabbun yan Boko Haram sun tare hanya suna zanga-zanga kan N30,000 a Borno: Hoto: @Zagazola
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Ganin Tulin Jami'an Tsaro Ya Jawo Mutane Sun Shiga Dar-Dar a Arewacin Najeriya

Da yake martani, Farfesa Usman Tar, kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, ya ce za a cigaba da tantance su bayan faruwar lamarin.

Ya ce bayan an samu daidaito, jami'an gwamnatin Borno sun cigaba da aikin tantance tubabbun yan Boko Haram din.

Kalli bidiyon zanga-zangan da tubabbun yan Boko Haram din suka yi

Jimillar tubabbu 6,900 ake tantancewa karkashin tsarin DDDRRR da aka fi sani da "Borno Model"

Kwararrun masu bincike da masana adana bayanai a na'ura mai kwawalwa aka dauka don gudanar da aikin cikin rukuni 6 don samun sahihan bayanai.

Sai dai, saboda kutsen hanyoyin sadarwa, wanda ya kamata a tantance daga baya ne suka bayyana yau, Juma'a, 18 ga watan Agusta, 2023, wanda hakan ya janyo rudani a inda ake gudanar da aikin tantancewar.

"Gwamnatin Jihar Borno na son bai wa al'umma tabbacin cewa an shawo kan lamarin kuma ana cigaba da tantancewar," in ji shi.

Lamarin ya nuna yadda hukumomi ke kokarin ganin ta mayar da tubabbun cikin mutanen gari bayan shafe shekaru 13 ana kai hare-hare da garkuwa da mutane da sunan jihadin musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164