Jami’an Kwastam Sun Kama Mazakutan Jakuna Na Fiye Da Biliyan 1 A Legas

Jami’an Kwastam Sun Kama Mazakutan Jakuna Na Fiye Da Biliyan 1 A Legas

  • Hukumar Kwastan ta cafke busassun mazakutan jakuna a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas
  • Hukumar ta kuma kama busassun kasusuwan kifaye 1700 da ake shirin ketarawa da su kasar Sin
  • Kwanturolan hukumar a filin jirgin, Mohammed Yusuf ya ce sun kama kayayyakin ne da ake kokarin ketarawa da su da su ka kai Naira biliyan 1.23

Jihar Legas - Hukumar Kwastam da ke filin tashi da saukan jiragen sama na Murtala Mohammed a Legas ta kama mazakutan jakuna da kayoyin manyan kifaye.

Hukumar ta kama wadannan kayan ne wanda jimillar kudin su su ka kai Naira biliyan 1.23 a ranar Alhamis 17 ga watan Agusta a Ikeja.

Kwastam ta kama busassun mazakutan jakuna a jihar Legas
Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu Na Mazakutan Jakuna A Legas. Hoto: Concise News.
Asali: Facebook

Meye Kwastam ta kama?

Da yake magana da 'yan jaridu, kwanturolan hukumar na shiyya, Muhammad Yusuf ya ce sun kama kayan ne yayin da ake kokarin fitar da su kasar Sin da kuma Hong Kong.

Kara karanta wannan

Boko Haram Ta Cafke 'Yan Kungiyar ISWAP 57 Da Kwamandojinsu 3 A Matsayin Fursunonin Yaki, Ta Bayyana Matakin Gaba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce hukumar ta samar da kudaden shiga har Naira biliyan 47.24 tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na 2023.

Yayin da aka samu Naira biliyan 40.35 a shekarar da ta gabata wanda hakan ke nuna karin kusan kashi 84, cewar Tribune.

Ya ce ana samar da mazakutan jakunan ne a birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi daga wani dan kasar Sin inda ya ce dole a kare jakunan daga bacewa a doron kasa.

Meye Kwastam ke cewa game da kamen?

Ya ce:

"Hukumar ta samu gagarumar nasara wurin kwato kayayyakin tare da taimakon wasu hukumomi.
"Mun kwace busassun kayoyin manyan kifaye da kudin su ya kai Naira miliyan 221 da kuma busassun mazakutan jakuna na Naira biliyan daya.
"Jimillar kudaden duka sun kai Naira biliyan 1.23.
"A yanzu mu na da kasusuwan busassun kifaye fiye da dubu daya, inda ya ce idan aka ci gaba da haka musamman a kan jakuna to za a neme su a rasa a doron kasa.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Muhammed ya godewa jami'an hukumar da sauran masu taimakawa wurin dakile irin wadannan kayayyaki, cewar Daily Nigerian.

Kwastam Ta Kama Harsasai Fiye Da Dubu 1 A Ogun

A wani labarin, Hukumar Kwastam ta kama harsasai fiye da dubu daya a jihar Ogun.

Hukumar ta cafke harsashen ne a cikin buhunan shinkafa inda ta gargadi jama'a kan irin wannan aika-aika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.