Kungiyar NLC Ta Yi Fatali Da Shirin Ba Wa Gwamnoni Tallafin Naira Biliyan 5, Sun Fadi Dalili

Kungiyar NLC Ta Yi Fatali Da Shirin Ba Wa Gwamnoni Tallafin Naira Biliyan 5, Sun Fadi Dalili

  • Kungiyar Kwadago ta NLC ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan mika ragamar tallafin Naira biliyan biyar ga gwamnonin jihohi
  • Kungiyar tare da ta ‘yan kasuwa wato TUC ta bayyana cewa gwamnonin jihohi ba abin yarda ba ne da irin wadannan kudade
  • Su ka ce kudaden za su makale ne a hannun ‘yan siyasar jihohin daban-daban ba tare da talakawa sun ji kamshin su ba don cin gajiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta soki shirin mika Naira biliyan biyar na tallafi ga gwamnonin jihohi 36 a Najeriya.

Kungiyar ta ce gwamnonin ba abin yarda ba ne inda su ka ce gwamnonin kawai za su ba wa ‘yan siyasa ne a jihohinsu, Legit.ng ta tattaro.

NLC ta gargadi Tinubu kan ba wagwamnoni Naira bilyan biyar na cire talafi
Kungiyar NLC Ta Gargadi Tinubu Kan Yarda Da Gwamnoni Da Kudin Tallafi. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Meye kungiyar NLC ke zargi?

A baya dai an sha ba wa gwamnonin jihohi irin wadannan kudade don rabawa talakawa amma kuma su ka mamaye kudin tare da ba wa wasu ‘yan tsiraru da su ke da alaka da su.

Kara karanta wannan

Murna ta Koma Ciki, Kudin Tallafin da Tinubu Zai ba Jihohi bashi ne ba Kyauta ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis 17 ga watan Agusta, Gwamnatin Tarayya ta sanar da ware Naira biliyan biyar ga jihohi 36 na kasar da kuma ware tireloli 180 na shinkafa don rage radadin yunwa.

Gwamnatin Tarayyar ta ware Naira biliyan 180 don rabawa jihohi 36 Naira biliyan biyar don rage radadin cire tallafi.

Tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi, ‘yan kasar su ka shiga mawuyacin hali.

Cire tallafin ya jawo hauhawan farashin kayayyaki da kuma tsadar mai din da ta jefa ‘yan Najeriya cikin wani irin yanayi, cewar Premium Times.

A kan meye NLC su ka yi zanga-zanga?

Kungiyar NLC a kwanakin baya ta yi zanga-zanga kan hauwawan farashin kaya a kasar da kuma neman Tinubu ya gyara matatun mai a kasar.

Kara karanta wannan

Komai Ya Lafa, Majalisa Ta Fadi Inda Aka Samo Miliyoyin ‘Hutun’ da Aka Biya Sanatoci

Saboda tsananin yunwa da wahalhalu a jiya Alhamis 17 ga watan Agusta wasu matan aure sun yi zanga-zanga a Rigasa da ke karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna.

Zanga-zangar an yi ta ne don nuna damuwa kan irin halin kunci da ake ciki na tsananin yunwa da tsadar abinci a kasar baki daya.

Matan auren sun roki Shugaba Tinubu da ya yi gaggawar daukar mataki don kawo sauyi da zai taimaka wurin rage tashin farashi musamman na abinci a kasar.

Cire Tallafi: Tinubu Ya Amince Da Raba N5bn Ga Jihohi

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya ware Naira biliyan 180 don raba wa jihohi 36 na fadin kasar.

An ware wadannan kudade ne don rage radadin cire tallafin mai ga 'yan kasar da su ka sha fama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.