Mataimakin Gwamnan Neja Ya Ce Jihar Na Da 'Yan Gudun Hijira Sama Da 5,000
- An bayyana cewa akwai aƙalla mutane 5,000 da suke gudun hijira a jihar Neja
- Mataimakin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayyana hakan a ofishin hukumar NEMA da ke Abuja
- Ya ce gwamnatin jihar na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta taimakawa mutanen da ke gudun hijirar
Abuja - An bayyana cewa a yanzu haka akwai mutane sama da 5,000 da ke gudun hijira sakamakon hare-haren 'yan bindiga a jihar Neja.
Mataimakin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyara ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Akwai 'yan gudun hijira 5,000 zuwa 6,000 a Neja
Mataimakin gwamnan na Neja ya shaidawa shugaban hukumar ta NEMA, Mista Mustapha Ahmed cewa hare-haren 'yan ta'addan da ake yawan samu a jihar ne ya janyo ƙaruwar 'yan gudun hijirar.
Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Ba Alkalai Cin Hancin N10m, Ta Bayar Da Dalilai
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce yanzu haka akwai 'yan gudun hijira da yawansu ya kai 5,000 zuwa 6,000 a jihar, kuma ana ci gaba da ƙara samun ƙaruwarsu.
Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa duk da yawan 'yan gudun hijirar da suke da su, suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun taimaki kowanensu daidai gwargwado.
Dalilin ziyarar mataimakin gwamnan Neja zuwa ofishin NEMA
Mista Yakubu ya bayyana maƙusudin ziyarar ta sa ofishin NEMA domin zayyanawa hukumar wasu abubuwa da suke damun jihar Neja tun shekaru shida zuwa bakwai baya.
Ya ce matsalar tsaro ce ta farko cikin matsalolin da suka fi addabar jihar, wacce ba a gama da ita ba kuma sai ga matsalar ambaliyar ruwan sama kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.
Ya ce ya zo ofishin na NEMA ne domin bai wa hukumar bayanai da kuma duba yadda za ta haɗa gwiwa da hukumar agajin jihar Neja wajen ganin a kai wa al'ummar jihar ɗauki.
Mataimakin gwamnan ya kuma shawarci mutanen da ke zaune a wuraren da ke cikin kwari da su koma kan tudu domin gujewa asarar rayuka da dukiyoyi daga ambaliyar ruwa.
Gwamnan Neja na shirin gyara sufurin jiragen saman jihar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ƙoƙarin da gwamnan jihar Neja, Umar Mohammed Bago yake yi na ganin ya gyara hada-hadar sufurin jiragen saman jihar.
Gwamnan ya ce ya fara tattaunawa da kamfanonin jigilar jiragen sama domin ganin an fara gudanar da zirga-zirga a filin jiragen saman jihar da ke Minna.
Asali: Legit.ng