Korafi Zai Kare, Tinubu Ya Amince a Raba wa Kowacce Jiha N5bn Na Rage Radadin Cire Tallafin Mai
- Gwamnatin tarayya ta amince da warewa kowace jiha naira biliyan 5 domin rage radadin cire tallafin man fetur
- Gwamna Babagana Zulum ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis, 17 watan Agusta bayan taron majalisar tattalin arziki na kasa
- Babban birnin tarayya Abuja ma za ta samu kaso a shirin da gwamnatin tarayya ke yi na magance mawuyacin halin da al'umma suka shiga saboda cire tallafin
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin raba wa kowacce jiha ciki harda babban birnin tarayya Abuja, tallafin naira biliyan 5, domin rage radadin cire tallafin man fetur, jaridar The Cable ta rahoto.
Gwamnati tarayya za ta warewa kowacce jiha biliyan 5 na cire tallafin mai
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ne ya bayar da sanarwar a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, lokacin da ya zanta da manema labarai na fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar tattalin arziki na kasa.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci zaman majalisar tattalin arzikin kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majalisar ta kunshi gwamnonin jihohi 36, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da sauran jami'an gwamnati, rahoton Punch.
Abubuwan da za a tattauna a taron majalisar tattalin arziki
Tun farko dai Legit.ng ta tattaro wasu batutuwa da za a tattauna a wajen taron NEC na yau, ana sa ran za a tattauna batutuwan da suka shafi halin da lalitar Gwamnatin Tarayya ke ciki da kuma sauran ƙarin matsalolin da suka shafi ƙasa.
Sai dai abu mafi muhimmanci da majalisar tattalin arziƙin za ta tattauna akai shi ne yadda za a gabatar da rabon kayan tallafi da za a bai wa 'yan Najeriya.
Za a ba da kayayyakin tallafin ne saboda ragewa 'yan ƙasa raɗaɗin da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ya jefa su a ciki.
Shehu Sani ya ce an fi tafka barna a CBN karkashin Buhari
A wani labari na daban, mun ji a baya cewa tsohon dan majalisar mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cibiyar da ta fi kowace aikata zamba a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sani ya ce babban bankin Najeriya (CBN) shine cibiyar gwamnati mafi damfara a tarihin Najeriya.
Asali: Legit.ng