Remi Tinubu Ta Yi Kira Ga 'Yan Najeriya Su Daina Jiran Sai Gwamnati Ta Yi Musu Komai

Remi Tinubu Ta Yi Kira Ga 'Yan Najeriya Su Daina Jiran Sai Gwamnati Ta Yi Musu Komai

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta aike da saƙo mai muhimmanci ga ƴan Najeriya kan su daina jiran sai gwamnati ta yi musu komai
  • Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana cewa lokacin kalmashe ƙafafuwa a jira sai gwamnati ta yi komai a ƙasar nan ya wuce
  • Remi ta yi kira ga mata da su tashi tsaye wajen ganin sun cusa tarbiyya mai kyau a zukatan matasa masu tasowa

FCT, Abuja - Remi Tinubu, uwargidan shugaban ƙasa Bola Tinubu, ta janyo hankalin ƴan Najeriya.

Uwargidan shugaban ƙasan ta bayyana cewa lokaci ya wuce da ƴan Najeriya za su kalmashe ƙafafunsu, su jira sai gwamnati ta yi musu komai.

Remi Tinubu ta shawarci yan Najeriya
Remi Tinubu tare da shugabannin NCWS Hoto: @KukoyiBusola
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana hakan ne, a jiya Laraba lokacin da ta karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar National Council for Women Societies (NCWS), a ofishinta da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

"Ba za mu jira sai gwamnati ta yi mana komai ba. Dole sai mun taimaki duk mutanen da mu ke rayuwa tare da su." A cewarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Remi ta yi muhimmin kira ga mata

Remi Tinubu ta buƙaci mata su tabbatar da cewa an ɗora matasa sun bi turbar halaye masu kyau da tarbiyya ta gari.

Ta yi nuni kan buƙatar mata su tashi tsaye wajen raba matasa da abubuwan rashin daraja da suka zama ruwan dare a soshiyal midiya a wannan lokacin.

Da take na ta jawabin, jagoran tawagar kuma shugabar ƙingiyar, Hajiya Lami Adamu Lau, ta bayyana cewa NCWS za ta yi haɗaka da uwargidan shugaban ƙasar kan shirin ta na 'Renewed Hope Initiative'.

Patience Jonathan ta ziyarci Remi

A halin da ake ciki, tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Patience Jonathan, a jiya Laraba ta ziyarci Remi Tinubu, inda ta yi mata alƙawarin bayar da gudunmawa wajen cimma manufofin taimakon marasa ƙarfi a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Ya Fadawa Tinubu Abinda Zai Faru Idan Bai Yi Maganin Halin Da Ake Ciki Ba

Ta bayyana cewa yana da matuƙar muhimmanci a matsayinta na tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa ta marawa Remi Tinubu baya akan abubuwan da za su kawo cigaba a ƙasa.

Lokacin Da Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa

A wani labarin kuma, fadar shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske kan lokacin da Shugaba Tinubu zai rantsar da ministocinsa.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya bayyana cewa shugaban ƙasar zai rantsar da ministocinsa a ranar Litinin mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng