Yan Bindiga Sun Farmaki Wata Coci a Jihar Edo, Sun Halaka Matar Faston Cocin
- Miyagun Ƴan bindiga sun halaka matar wani sanannen fasto a birnin Benin, babban birnin jihar Edo a wani hari
- Miyagun sun kai hari cocin God’s Vineyard of Grace Dominion Assembly, inda suka farmaki Rev. Samuel Chinyereugo, da halaka matarsa Mrs. Peace Chinyereugo
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin sannan ta fara gudanar da bincike kan harin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Benin, jihar Edo - Ƴan bindiga sun kai hari a cocin 'God’s Vineyard of Grace Dominion Assembly', inda suka farmaki faston cocin Rabaran Samuel Chinyereugo, a birnin Benin babban birnin jihar Edo.
A yayin harin, ƴan bindigan sun harbi matarsa, Mrs. Peace Chinyereugo, wacce ta mutu a sakamakon harbin, cewar rahoton PM News.
Lamarin dai ya auku ne a ranar Litinin, 14 ga watan Agustan 2023, a harabar cocin da ke a layin Upper Lawani Street, New Benin, a cikin birnin Benin.
Shaidun gani da ido sun yi bayani
A cewar shaidun gani da ido, babban faston wanda ya je ziyarar wnai abokinsa a GRA, ƴan bindigan sun biyo sahunsa ɓe har zuwa cocin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma suna kusa wajen cocinsa, sai suka sha kan motar faston suka hana shi wucewa.
Ƴan bindigan waɗanda su uku ne, suna sauka daga motarsu kawai sai suka buɗe wuta kan faston, matarsa da wani mataimakinsa wanda ba a bayyana sunansa ba.
An garzaya da su zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, inda likitoci suka tabbatar da matar faston ta mutu.
Ƴan sanda sun yi martani
Da yake magana kan harin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da kisan, ya bayyana cewa ba a cafke kowa ba har ya zuwa yanzu.
Sai dai, ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu akan harin, rahoton New Telegraph ya tabbatar.
'Yan Bindiga Sun Sace Ma'aurata a Jihar Ebonyi
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aurata da ɗiyar si tare da direban su a jihar Eɓonyi da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Ƴan bindigan sun ritsa mutanen ne lokacin da su ke kan hanyar su ta zuwa unguwa, inda suka tasa ƙeyar su zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng