Dangote Ya Fice Daga Jerin Attajirai 100 Na Duniya Bayan Ya Yi Asarar N36bn

Dangote Ya Fice Daga Jerin Attajirai 100 Na Duniya Bayan Ya Yi Asarar N36bn

  • Aliko Dangote ya yi asarar N36bn a dukiyarsa, wanda hakan ya sanya ya rasa matsayinsa a cikin attajirai 100 na duniya
  • Duk da har yanzu shi ne attajirin da ya fi kowa a duniya, dukiyar Dangote ta yi ƙasa tun lokacin da CBN ya karya darajar naira
  • Attajirin ƙasar Afirika ta Kudu, Johann Rupert wanda shi ne attajiri na biyu da ya fi kowa kuɗi a Afirika, ya rasa sama da $200m a kwana ɗaya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika sama da shekara 10 baya, ya fita daga cikin jerin attajiran duniya 100.

Hakan ya biyo bayan asarar da ya tafka ta N36.72bn (ku san $47.5m) daga cikin dukiyarsa cikin ƴan sa'o'i a ranar Laraba, 16 ga watan Agustan 2023.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Arzikin Dangote ya ragu da N36bn
Dangote ya yi asarar N36bn cikin yan sa'o'i Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

A cewar Bloomberg, arziƙin Dangote ya ragu zuwa $16.9bn, inda yanzu ya koma attajiri na 101 cikin jerin attajiran duniya.

Daga watan Janairu zuwa ranar 16 ga watan Agusta na wannan shekarar, Dangote ya tafka asarar da ta kai ta $1.83bn a dukiyarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Attajirin ƙasar Afirika ta Kudu, Johann Rupert, wanda shi ne attajiri na biyu ma fi kuɗi a nahiyar Afirika da dukiyar da ta kai $12.2bn, ya yi asarar sama da $230m.

Rupert shi ne attajiri na 149 daga cikin masu kuɗin duniya, inda yake a ƙasan Dangote da matakai 48.

Inda Dangote yake samo dukiyarsa

Ma fi yawa daga arziƙin Dangote yana zuwa ne daga hannun jarin kaso 86% da yake da shi a kamfanin simintin Dangote.

Yana riƙe da hannun jarin kamfanin ne ta hannun rukunin kamfanunnikan Dangote.

Kara karanta wannan

'Da Karfi Ya Zo': Dangote Ya Karbi Matsayinsa Na Mafi Kudi A Afirka Da Ribar N13bn, Forbes Ta Yi Bayani

Sauran kamfanonin da yake da hannun jari sun haɗa da Dangote Sugar, Nascon Allied Industries, da bankin United Bank for Africa (UBA).

Dangote yana da sauran harkokin kasuwanci da yake gudanarwa a fannin sarrafa abinci, takin zamani, man fetur da sauran su.

Kamfamin NNPC Ya Ciyo Bashi

A wani labarin kuma, kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya ciyo bashin dala biliyan uku ($13bn).

Kamfanin ya ciyo bashin ne daga bankin AFRIEXEM domin daidaita darajar naira wacce take ta shan kashi a hannun dala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng