Kamfanin NNPC Ya Ciwo Bashin Dala Biliyan 3 Don Gyara Farashin Naira

Kamfanin NNPC Ya Ciwo Bashin Dala Biliyan 3 Don Gyara Farashin Naira

  • Kamfanin NNPC ya ciwo bashin Dala biliyan uku a wani bankin kasar Masar don inganta farashin Naira a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan Naira ta fadi warwas a kwanan nan a Najeriya yayin da Dala ta yi mummunan ta shi
  • Hadimin Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ya bayyana amfanin karbar bashin da cewa zai inganta Naira tare da saukar da farashin mai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kamfanin mai na NNPC ya ciwo bashin Dala biliyan uku don kawo daidaito a darajar Naira.

Kamfanin ya samu nasarar ciwo bashin ne a bankin AFRIEXIM da ke birnin Cairo a kasar Masar.

NNPC ta ci bashin Dala biliyan 3 don inganta Naira a kasar
Kamfanin NNPC Ya Runtumo Bashin Dala Biliyan 3 A Kasar Masar Don Inganta Naira. Hoto: NNPC.
Asali: UGC

NNPC ya tabbatar da haka ne a cikin wata sanarwa a yau Talata 16 ga watan Agusta, TheCable ta tattaro.

Meye amfanin bashin NNPC ga Najeriya?

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 2, Bola Tinubu Ya Yi Fatali da Tsarin da CBN Ya Kawo a Mulkin Buhari

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a biya bashin ne da danyen mai da kudin ruwan da bai wuce kashi takwas zuwa 11 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Kamfanin NNPC da bankin AFRIEXIM sun yi hadaka don karbar bashin gaggawa har Dala biliyan uku.
"Za a yi amfani da kudaden wurin daidaita farashin Naira da kasuwar 'yan canjin kudade.
"Bashin da aka karba za a biya ne da danyen mai daga kamfanin NNPC."

Meye hadimin Tinubu ya ce game da bashin NNPC?

Yayin da ya ke martani, Ajuri Ngelale wanda hadimi ne ga shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce wannan mataki zai kara taimakawa Naira don dawo da martabar ta.

Ya ce a duk lokacin da aka samu Naira ta kara daraja, a lokacin ne kuma farashin mai ke kara kasa.

Wannan bashi zai taimakawa Najeriya daga karbar bashin Hukumar Ba Da Lamuni ta IMF, sannan zai kara wa Naira daraja wanda ta sha wuta a hannun Dalar Amurka a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

Naira ta fadi warwas a ranar Juma'a 11 ga watan Agusta zuwa Naira 950 a kan ko wace Dala daya, cewar Vanguard.

Dala Ta Fado Kasa Warwas Bayan Ganawar Tinubu Da Gwamnan CBN

A wani labarin, Dalar Amurka ta fadi warwas bayan mummunan tashi da ta yi 'yan kwanakin nan da kusan N950.

Amma a yanzu haka rahotanni sun tabbatar cewa ana siyan Dalar N790 zuwa N805 a kasuwannin canji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.