Bayan Haduwan Tinubu da Gwamnan CBN, Naira Ta Na Farfadowa Kan Dalar Amurka

Bayan Haduwan Tinubu da Gwamnan CBN, Naira Ta Na Farfadowa Kan Dalar Amurka

  • A sakamakon tallafin da bankin CBN ya ba ‘yan canji, Dalar Amurka ta fara rage daraja a yanzu
  • Tun da aka daidaita kudin kasashen waje, aka rasa yadda za a hana Naira karyewa a kan Dala
  • Tun ba yanzu ba, Folashodun Shonubi ya nuna babban bankin bai yarda da yadda Naira ta ke tashi ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Dalar Amurka ta fado kasa a kasuwar canji bayan wani mummhunan tashi da farashin ta ya yi a ‘yan kwanakin bayan nan.

A safiyar Laraba, Daily Trust ta fitar da rahoto cewa yanzu maganar da ake yi, ana saye da saida Dala tsakanin N790 zuwa N805.

Dalar Amurkan da mutane su ka rika samu a kan N925 zuwa N930 kafin yanzu, ta sauka zuwa kasa N800 a wasu wuraren a yau.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zauna da Gwamnan CBN Sakamakon Tsinkewar Farashin Dala a Kasuwa

Dalar Amurka
Dalar Amurka ta sauko Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan canji sun samu Dala?

Ana kyautata zaton Naira ta mike ne bayan tallafin da bankin CBN ya kai wa ‘yan canji na BDC, a yayin da ake fama da matsin lamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kasuwannin Allen Avenue da Bagada da ke garin Legas, ‘yan canji sun koma saida Dalar a kan N900 zuwa N910 a maimakon N970.

Rahoton ya ce kudin na Najeriya ya kara daraja da fiye da N60 a cikin ‘yan awanni a kasuwa.

Nawa Dala ta koma a yau?

Masu saida Dalar Amurkan a kasuwar Wapa da ke jihar Kano, su na saida duk $1 a kan N905, idan mutum zai saida $1, za a biya shi N875.

Idan aka koma Abuja, a kan N789/$ ake saida kudin kasar wajen a kafar I & E da bankin CBN ya fito da shi domin masu ciniki a ketare.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Babban bankin ya saida Dala a kan kusan N800 kafin yanzu, yanzu kuwa za a iya samun ta a kan N740, hakan ya nuna Naira ta mike kadan.

"An fara mana yanga"

Wani Abdullahi Adamu a jihar Kaduna, ya shaida mana Dalar ta fara karyewa a kasuwa.

A cewarsa masu canji sun fara yi masa yanga yayin da yake so ya saida wasu ‘yan dalolinsa, a cewarsa farashin Dalar ya sauko a makon nan.

Bola Tinubu v Folashodun Shonubi

Dama can Gwamnan babban banki, Mista Folashodun Shonubi ya bada sanarwar cewa za su yi hobbasa domin ganin Dala ta rage tsada.

Folashodun Shonubi ya sha wannan alwashi ne bayan wata ganawa da ya yi da Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin a fadar Aso Rock Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng