'Yan Bindiga Sun Halaka Sabbin Ma'aurata a Jihar Plateau
- Rwang Danladi da Sandra Rwang Danlaɗi sun gamu da ajalinsu a hannun miyagin ƴan bindiga a jihar Plateau
- Mutanen biyu sun mutu ne bayan ƴan bindigan sun buɗe musu wuta a makarantar da su ke koyarwa
- Ƴan bindigan sun kuma yi wa mataimakin shugaban makarantar mummunan rauni a lokacin da suka kawo harin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun halaka wasu malaman makarantar sakandire mutum biyu na makarantar Beco Comprehensive High School a ƙauyen Kwi cikin ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau.
Malaman biyu da aka halaka, Rwang Danladi da Sandra Rwang Danladi, ba a daɗe da ɗaura musu aure ba, cewar rahoton Channels tv.
Kakakin ƙungiyar Berom Youths Moulder-Association (BYM), Rwang Tengwong, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ranar Talata, ya ce an halaka malaman ne a ranar Litinin lokacin da malaman makarantar ke taro kan shirye-shiryen bikin yaye ɗalibai da za su yi a ranar Juma'a.
An zargi Fulani da kai harin
Ƙungiyar ta zargi Fulani makiyaya da halaka malaman, inda ta ce sun buɗe wuta kan malaman makarantar bayan sun buƙaci da su bar harabar makarantar lokacin da su ke gudanar da taron su, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rwang ya bayyana cewa:
"Ƴan bindigan sun shigo cikin harabar makarantar tare da dabbobinsu, inda suka hana taron malaman. Malaman sun buƙace su da su ɗauke dabbobinsu daga cikin harabar makarantar. Amma a maimakon su yi hakan, sai suka ciro bindigu suka buɗe musu wuta."
"Hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wasu sabbin ma'aurata biyu, Rwang Danladi da matarsa Sandra Rwang Danladi, waɗanda malaman makarantar ne, yayin da Dalyop Emmanuel Ibrahim wanda shi ne mataimakin shugaban makarantar ya samu rauni inda ake duba lafiyarsa a asibiti."
Ƴan sanda ba su ce komai ba
Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau, DSP Alabo Alfred, bai ce komai ba kan saƙon da aka aike masa domin jin ta bakinsa dangane da lamarin.
'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyu a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun halaka wasu bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Plateau.
Mutanen biyu da ƴan bindigan suka halaka ƴan kasuwa waɗanda ke kan hanyat su ta komawa gida bayan sun je kasuwa a ƙauyen Kinat na ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.
Asali: Legit.ng