Matashi Ya Yi Layar Zana Da Motar Miliyan 23 Da Aka Ba Shi Wanki, An Saki Hotonsa a Soshiyal Midiya

Matashi Ya Yi Layar Zana Da Motar Miliyan 23 Da Aka Ba Shi Wanki, An Saki Hotonsa a Soshiyal Midiya

  • An fara farautar wani matashi da ya tsere da motar naira miliyan 23 da aka ajiye a karkashin kulawarsa a soshiyal midiya
  • Legit.ng ta tattaro cewa an nemi matashin ya wanke motar ne a Lagas amma tun lokacin ba a sake ganinsa ba
  • Hotunan barawon motar da tsadaddiyar motar da aka sace ya bayyana a soshiyal midiya inda mutane suka yi martani kan lamarin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani ma'aikaci da ba a san ko wanene ba ya tsare da motar ubangidansa da aka ba shi ajiya wanda ya kai naira miliyan 23 a jihar Lagas.

An bukaci matashin da ya wanke motar ne a wani wajen wankin mota da ke unguwar Abraham Adesanya, Lagas.

Matashi ya arce da motar miliyan 23 da aka ba shi wanki
Matashi Ya Yi Layar Zana Da Motar Miliyan 23 Da Aka Ba Shi Wanki, An Saki Hotonsa a Soshiyal Midiya Hoto: Amanda Chisom
Asali: Facebook

Wata ‘yar jarida mai suna Amanda Chisom ta bayyana batun satar da aka yi a Facebook kuma ta ce ta same shi ne a akwatin sakonta.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2, Ciki Harda Jaririn Kwana Daya

Yayin da take wallafa hotunan motar da wanda ake zargin ya yi satar, ta bayyana sakon da aka aike mata kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina kwana, don Allah ki taimaka mana wajen yada wannan, wani ma'aikaci ya tsere da motar miliyan 23 da aka bari a karkashin kulawarsa domin ya wanke a wajen wanke motoci a Abraham Adesanya Lagas."

Jama'a sun yi martani a kan labarin satar mota

Chukwudi Vincent Okafor ya ce:

"Mutane sai magana suke kan dalilin da yasa ba a sa na'urar bin diddigi a motar sai ka ce ba mutane ne ke sanya ita na'urar ba. Muna da shiri kan abun da muka shiryawa sosai kafin mu aiwatar da shi."

Chiamaka Favour Nzeh ta ce:

"Duk mutanen nan da ke tambayar dalilin da yasa basu sa na'urar bin diddigi ba, shin basa ganin motar na kasuwa ne, Allah ya kyautawa wasu mutane, ya kuke so su saka na'urar bin diddigi."

Kara karanta wannan

Asara: Matsafa Sun Kashe Malamin Addini A Gonarsa Bayan Yin Basaja A Matsayin Leburori, 'Yan Sanda Sun Yi Bayani

Shehu Sani ya bayyana cibiyar gwamnati da ta fi zamba a mulkin Buhari

A wani labarin, mun ji cewa tsohon dan majalisar mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cibiyar da ta fi kowace aikata zamba a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sani ya ce babban bankin Najeriya (CBN) shine cibiyar gwamnati mafi damfara a tarihin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng