Najeriya Ta Zama Kasa Ta 3 a Jerin Kasashen Nahiyar Afirika Da Ake Turanci Mai Kyau
- Najeriya ta samu matsayi a wata sabuwar ƙididdiga kan kasashen da suka iya turanci na manuniyar 'Education First English Proficiency Index' (EF EPI) da aka fitar
- A cewar sabuwar ƙididdigar, Najeriya ita ce ƙasa ta uku a nahiyar Afirika da ake Turanci mai kyau kuma ƙasa ta 28 a duniya
- Najeriya ta zo ta uku inda take a bayan ƙasashen Afirika ta Kudu da Kenya waɗanda suka zo na ɗaya da na biyu a cikin jerin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Najeriya ta zama ƙasa ta uku inda ake yin yaren Turanci mai kyau a nahiyar Afirika sannan ƙasa ta 28 a duniya.
A cewar rahoton ƙididdigar gwanancewa wajen Turanci da aka sanya a shafin 'Education First English Proficiency Index EF EPI', Najeriya ta samu matsayin ne a ƙididdigar ƙasashen da ake Turanci mai kyau 111 da aka gudanar a shekarar 2022.

Kara karanta wannan
Kungiyoyin Kwadago NLC Da TUC Sun Sha Alwashin Tsunduma Yajin Aiki Idan Aka Kara Farashin Litar Man Fetur

Source: Getty Images
Najeriya ta zama ƙasa ta uku inda ake Turanci mai kyau a Afirika
Najeriya ta zama ta uku a cikin jerin ƙasashen da ake Turanci mai kyau a nahiyar Afirika. Ƙasar Afirika ta Kudu ta zo ta ɗaya yayin da ƙasar Kenya ta zo ta biyu a cikin jerin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ƙasar Afirika ta Kudu ta zo ƙasa ta 12 a duniya inda ake Turanci mai kyau yayin da ƙasar Kenya ta zo ta 20 a cikin jerin.
Ƙididdigar ta nuna ƙasashen nahiyar Afirika 20 sun samun shiga cikin jerin ƙasashen da ake Turanci mai kyau a duniya.
Sauran ƙasashen sun haɗa da Ghana ta huɗu a Afirika sannan ta 41 a duniya, sannan sai ƙasar Uganda ta biyar a Afirika kuma ta 55 a duniya.
Ga jerin ƙasashen Afirika 20 da suka shiga cikin ƙasashen da ake Turannci mai kyau.

Kara karanta wannan
Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Soye 'Yan Ta'adda Masu Yawa a Arewacin Najeriya a Wani Luguden Wuta Da Suka Yi Musu
1. Afirika ta Kudu (12 a duniya)
2. Kenya (20 a duniya)
3. Najeriya (28 a duniya)
4. Ghana (41 duniya)
5. Uganda (55 duniya)
6. Tunisia (56 a duniya)
7. Tanzania (63 a duniya)
8. Ethiopia (68 a duniya)
9. Morocco (76 a duniya)
10. Algeria (78 a duniya)
11. Egypt (85 a duniya)
12. Mozambique (86 a duniya)
13. Sudan (95 a duniya)
14. Cameroon (96 a duniya)
15. Somalia (100 a duniya)
16. Côte d’Ivoire (104 a duniya)
17. Angola (105 a duniya)
18. Rwanda (107 a duniya)
19. Libya (108 a duniya)
20. Democratic Republic of Congo (110 a duniya).
Masu HND Za Su Samu Kwalin Digiri
A wani labarin kuma, hukumar ilmin ayyukan hannu (NBTE) ta ƙaddamar da shirin karatun mayar da kwalin HND zuwa na digiri.
A wannan sabon karatun wanda za a yi cikin shekara ɗaya, masu kwalin HND za su samu kwalin digiri bayan sun kammala.
Asali: Legit.ng