Ana Sukar Sanatoci, CBN Ya Cinye Naira Biliyan 155 a Alawus din Ma'aikata a 2022
- Ma’aikatan bankin CBN sun lakume alawus da bashin Biliyoyin kudi daga shekarar 2016 zuwa 2022
- CBN ya rika biyan alawus na Naira biliyan 100 ga ma’aikata a kasar da wasu ke karbar albashin N38, 000
- Wannan ya faru ne a Gwamnatin Muhammadu Buhari, a lokacin Godwin Emefiele ya na Gwamnan bankin
Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN ya ce alawus da aka biya ma’aikata a shekarar 2022 kurum ya haura Naira biliyan 155.63.
Wani labari da The Cable ta fitar ya yi bayanin kudin da babban bankin kasar ya kashe a tsawon shekaru bakwai daga 2016 zuwa 2022.
Bankin ya fitar da rahoton kudin a shafinsa na yanar gizo a karshen makon jiya, kwanaki bayan an ji za a gudanar da bincike a bankin.
Kafin a batar da wadannan makudan kudi, bankin ya ce majalisar da ke kula da shi ta amince da hakan kamar yadda dokar 2007 ta tanada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani alawus ake samu a CBN?
Jaridar ta ce ma’aikata sun karbi alawus iri-iri da su ka hada da na kayan daki da kudin gida a Najeriyar da fetur yake neman ya gagara.
Sauran alawus da ma’aikatan babban bankin su ka tashi da shi a tsawon lokacin ya hada da na tafiya, daukar hutu, da na yin aiki da kyau.
Bincike ya nuna Naira biliyan 155 da aka kashe ya zarce ribar Naira biliyan 65.63 da bankin ya ke takamar ya samu tsakanin 2016 da 2022.
CBN ya ba ma'aikata aron kudi
A shekarar 2021, abin da ma’aikatan na CBN su ka samu da sunan alawus shi ne Naira biliyan 113.35, bai kai kudin da aka ware a 2022 ba.
Har ila yau, daga rahoton kashe kudin da aka fitar, bankin ya ba ma’aikatansa bashin Naira biliyan 40.66 wanda za su rika biya sannu a hankali.
A yayin da ma'aikata ke rokon karin albashi, bankin bai iya yin cikakken bayani a kan wadanda su ka ci moriyar wannan bashi a lokacin ba.
A shekarar 1999, bankin ya na da ma’aikata 10, 000 amma sannu a hankali su ka yi ta rage yawa zuwa ma'aikata 6, 199 a karshen shekarar 2004.
Karin kudin man fetur
Rahoto ya zo cewa matuƙar dalar Amurka za ta tashi, dole ne farashin man fetur zai tashi sama, yanzu ana batun farashi ya karu da 37% a yau.
Dillalai ba su iya samun dala, idan aka je hannun ‘yan canji kuwa $1 ta haura N920 a yau, shiyasa ake tunanin man fetur zai iya komawa N720.
Asali: Legit.ng