Jerin Kamfanonin da Baku San Mallakin Babban Bankin Najeriya da Bayanai a Kansu

Jerin Kamfanonin da Baku San Mallakin Babban Bankin Najeriya da Bayanai a Kansu

  • A bayyane yake, Babban Bankin Najeriya (CBN) ne kololuwar tsarin banki da hada-hadar kudi a kasar baki dayanta
  • CBN dai ke kula da ba lasisin bakuna da yadda suke gudanar da ayyukansu a fadin kasar tare da rarraba kudade
  • Baya ga ayyukansa na dokar kudade da sauransu a Najeriya, akwai kamfanoni da CBN ke da jari ko kuma ya mallake

Kwanan nan ne Babban Bankin Najeriya ya fitar da rahotonsa na kudi na 2022 bayan shafe shekaru 7 ana jira, kuma akwai adadi mai kayatarwa.

Baya ga samun ribar sama da Naira biliyan 100, rahoton ya kuma bayyana cewa JP Morgan da Goldman Sachs na bin CBN kudaden da suka kai dalar Amurka biliyan 7.5, da dai sauransu.

Hakazalika, a cikin rahoton, CBN ya bayyana ayyukan rassansa daban-daban da kuma abubuwan da ya samar na kudade.

Kara karanta wannan

Ana Sukar Sanatoci, Ma’aikatan CBN Sun Cinye Naira Biliyan 260 a Alawus a Shekara 2

Kamfanon babban bankin CBN
CBN na da kamfanoni sama da 10 | Hoto: stears.co
Asali: UGC

Abubuwan da CBN ya mallak

1. NSPM

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban bankin na CBN ya mallaki kashi 89.52% na hannun jarin Kamfanin Buga Takardu na Najeriya.

Babban makasudin NSPM shine buga takardun kudin Najeriya da tsabar kudi tare da duk wasu takaddun tsaro da samfuran takardun gwamnati.

NSPM na kuma kerawa da shigo da tawadar bugun takardu da dai sauran abubuwan da ba a rasa ba.

2. NESI

Babban bankin na rike da 99.99% na hannun jari a kamfanin tsara rarraba wutar lantarki na NESI.

Wannan fanni yana aiki ne don habaka dorewa da ingancin masana'antar samar da wutar lantarki ta Najeriya.

Sauran inda CBN ke da hannun jari

Nigeria Deposit Insurance Corporation (NDIC): 60%

  1. AMCON: 50%
  2. Nigeria Interbank Settlement System (NIBSS): 3.6%
  3. FMDQ-OTC Plc: 15.4%
  4. Bank of Industry (BOI): 5.2%
  5. Bank of Agriculture (BOA): 14%
  6. National Economic Reconstruction Fund (NERFUND): 3.6%
  7. Nigeria Commodity Exchange (NCX): 59.7%
  8. Africa Finance Corporation: 42.4%
  9. Nigerian Export-Import Bank: 50%
  10. Agricultural Credit Guarantee Scheme Fund: 40%
  11. Nirsal Microfinance Bank: 40%

Kara karanta wannan

Dillalai Sun Tsaida Karin Kusan N100, Litar Fetur Za Ta Iya Komawa N680-N720

Za a fallasa masu harkallar Forex

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba da gargadi game da matakin da za a iya dauka kan cibiyoyin hada-hadar kudi da ke da hannu wajen siyar da daloli ba bisa ka’ida ba ko kuma hada-hadar kudi ba tare da izini ba.

Gargadin ya biyo bayan koma bayan da darajar Naira ta Najeriya ta samu kan dala a kasuwannin da gwamnati ta amince da su da ma na bayan fage.

Folashodun Shonubi, mukaddashin gwamnan CBN ne ya sanar da hakan a lokacin da yake gabatar da wata lacca mai taken a Abuja, NairaMetrics ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.