An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali

An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali

  • Watanni bayan daurin aurensu, an sha shagalin bikin Bello El-Rufai da kyakkyawar amaryarsa Aisha Shu'aibu
  • Bello ya kasance dan majalisa mai wakiltan mazabar Kaduna ta arewa kuma dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
  • Hotuna sun bayyana daga kasaitaccen bikin da aka yi a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta wanda ya samu halartan manya ciki harda Gwamna Uba Sani

Jihar Kaduna - An sha shagalin bikin Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma dan majalisa mai wakiltan mazabar Kaduna ta arewa a majalisar wakilai.

A watan Mayun shekarar nan ne aka daura auren Bello da amaryarsa Aisha Shuaibu a wani biki da aka yi cikin sirri a Abuja.

An sha shagalin bikin Bello El-Rufai da amaryarsa Aisha
An Sha Shagalin Bikin Dan Majalisar Kaduna, Bello El-Rufai Da Tsaleliyar Amaryarsa, Hotunan Sun Dauki Hankali Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Aisha ta kasance diya ga tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Filato da Neja, Kanal Habibu.

Kara karanta wannan

Kujerar Minista: Uba Sani Ya Magantu Kan Zargin Yi Wa El-Rufai Tuggu a Wurin Tinubu

Ku tuna cewa Bello ya auri matarsa ta farko Kamilah a shekarar 2015.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamilah ta kasance yar kanwar matar tsohon shugaban kasar Najeriya, Maryam Babangida, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamna Uba Sani ya taya ma'auratan murna

Da yake taya ma'auratan murna a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi masu fatan samun farin ciki a gidan aurensu.

Uba Sani shine ya tsaya a matsayin uban angon a wajen taron, kuma Bello ya kasance tsohon hadiminsa.

Ya rubuta a shafin nasa:

"A ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, 2023, na samu damar tsayawa a matsayin uban ango a wajen daurin auren tsohon babban mai taimaka min a majalisar dokoki, kuma dan majalisar wakilai (Mazabar Kaduna ta Arewa), Hon. Bello El-Rufai da kyakkyawar matarsa, Aisha Shuaibu.

Kara karanta wannan

WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista

"Ina musu fatan Alheri, kuma ina musu addu'ar Allah ya sanya ma aurensu albarka. Ameen"

Jama'a sun yi masu fatan alkhairi

@Mubescent ta yi martani:

"Ina yi musu fatan alkhairi a rayuwar aure."

@NasirShika ya ce:

"Masha Allah. Allah yasa Albarka."

@Funkemyfun ta ce:

"Ina taya ka murna Hon Bello."

@MansurYahaaya ya yi martani

"Allah ya bada zaman lafiya."

@usman_mai kyau ya ce

Ina taya ku murna. Allah ya albakaci gidanku."

@miibrahimhja ya ce:

"Masha allah,allah yasanya albarka."

@maimuna9523 ta ce:

"MashaAllah; Allah ya basu zaman lafiya."

Yadda hadadden likita ya rikirkita yan mata a intanet

A wani labarin kuma, wani hadadden likita ya saki zafafan hotunansa yana bakin aiki a soshiyal midiya.

Kyawun fuska da surar da Allah ya yi wa likitan ya rikirkita yan mata inda suka nuna sha'awar son mallakarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng