Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu Gaba Daya a Kano
- Gwamna Abba gida-gida ta jihar Kano ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu gaba daya a jihar
- Wannan na daga cikin matakin da gwamnati ke yi na tabbatar da makarantun sun cike tsari da ka'idoji domin samun ilimi mai inganci
- An umurci masu makarantun da su sake yin rijista da gwamnatin jihar domin sabonta lasisin su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin, Abba Kabir Yusuf, ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a fadin jihar.
Kamar yadda jaridar Kano Focus ta rahoto, mai ba gwamna shawara na musamman kan makarantu masu zaman kansu, Alhaji Baba Abubakar Umar ne ya sanar da hakan a wani taro da ya yi da mamallakan makarantun a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta.
Gwamnonin Arewa Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Masarautar Zazzau Kan Rushewar Masallaci Da Ya Yi Sanadiyar Rasa Rayuka
Alhaji Umar ya kuma bayyana cewa ana sa ran gaba daya makarantun za su koma su sake yin rijista domin sabunta lasisinsu, rahoton Aminiya.
Har ila yau, hadimin gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin Abba gida-gida na tsaftace ayyukan makarantu masu zaman kansu tare da tabbatar da sun bi tsari da ka’idoji.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnatin ta kuma bukaci masu makarantun da su biya kaso 10 na harajin da ke wuyansu a kan lokaci domin tabbatar da ci gaban bangaren ilimi a jihar.
'Gwamnatin Kano bata da niyan cin zarafin kowa', hadimin gwamna
Hadimin gwamnan ya kuma bukaci jama'a da kada su dauki wannan kokari da ake na dawo da tsarin kula da makarantu masu zaman kansu a matsayin barazana, a cewarsa, gwamnatin bata da niyar cin zarafin kowa.
Har ila yau, gwamnatin jihar ta bayyana kudirinta na daukar matakan da suka dace kan duk wata makaranta mai zaman kanta da aka samu ta keta wannan ka’ida.
Ya kuma bayyana cewa an samar da wata manhaja da za ta magance duk wata matsala daga bangaren gwamnati, masu makarantu, iyaye da ma masu neman aiki a makarantun, inda ya bai wa iyaye tabbacin kare muradunsu da yaransu.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar mamallaka makarantu masu zaman kansu na kasa reshen Jihar Kano, Alhaji Muhammad Malam Adamu, ya yaba da wannan mataki na gwamnatin domin a cewarsa hakan zai kara bunkasa harkar ilimi a jihar.
Gwamnatin Kano ta soke lasisin yan Kannywood gaba daya
A wani labari makarancin wannan, mun kawo a baya cewa gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin gaba daya yan masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
Kamar yadda shugaban kungiyar tantance fina-finai na jihar, Abba El-Mustapha ya bayyana, an dauki matakin ne domin tsaftace masana'antar da kuma cire baragurbi a cikinsu.
Asali: Legit.ng