Ban Taba Tattauna Batun Maye Gurbin El-Rufai da Tinubu Ba, Uba Sani Kan Batun Kujerar Minista

Ban Taba Tattauna Batun Maye Gurbin El-Rufai da Tinubu Ba, Uba Sani Kan Batun Kujerar Minista

  • Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa, ba za a ji tsakaninsa da wanda ya gada ba, Malam Nasiru El-Rufai ba
  • Uba Sani ya karyata labarin da ke cewa ya gana da Tinubu kuma ya ba da shawari kan nadin minista daga Kaduna
  • El-Rufai ya bayyana cewa, ba ya sha’awar yin minista a mulkin Tinubu saboda hassadar da ake ta yadawa a kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya musanta wani labari da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke cewa shi ya ki amincewa da sunan Nasir El-Rufai a matsayin minista daga jihar.

Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya zabi El-Rufai a matsayin minista amma har yanzu majalisar dattawa ba ta amince ba, inda ta ce akwai wasu korafe-korafen tsaro da ake yadawa a kan tsohon gwamnan na Kaduna.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Yadda Masu Rike da Madafan Iko Su ka yi wa El-Rufai Taron Dangi

An ce El-Rufai ya gana da Tinubu ya ce masa ba ya sha’awar zama minista a yanzu, kuma Jafaru Sani tsohon kwamishinansa ya shawarta a dauka a maye gurbinsa.

Uba Sani ya magantu kan alakarsa da El-Rufai
Uba Sani da Malam Nasiru El-Rufai | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bayanai daga ofishin gwamnan Kaduna

A ranar Asabar ne aka ruwaito Sani, magajin El-Rufai cewa ya gana da Tinubu ya ki amincewa da Jafaru a kan cewa shi mai biyayya ga El-Rufai ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya shaidawa jaridar TheCable cewa:

“Abin da yake gaskiya a cikin labarin shi ne na gana da shugaban kasa. Duk wani batu karya ne kuma kokari ne na haifar da rikici tsakanina da Mallam (El-Rufai).
“Na je ganin shugaban kasa ne musamman saboda na damu da yadda al’amura ke faruwa a yanzu. Na yi imani dukkansu biyu suna da fa’ida ga kasa.”

Ba a za ji ni da El-Rufai ba - Sani

Kara karanta wannan

WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista

Ya kara da cewa:

“Babu wani lokaci da muka tattauna batun maye gurbinsa. Wannan abu ne da bai dame ni ba.”
“Idan da gaske Mallam yana son ya zabi wanda zai maye gurbinsa, ba zan taba adawa da zabinsa ba. Muna kan tafarki daya. Wadanda suka san mu sosai sun san cewa wannan duk karya ce. Mun san daga ina aka samo wannan karya amma ba mu damu ba."

Ana kyautata zaton cewa wani tsohon dan majalisar dattawa daga jihar ne ke ta yada labarai a kafafen yada labarai domin haifar da rashin jituwa tsakanin Sani da El-Rufai.

El-Rufai ya daina sha'awar zama minista

Wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, ya bayyana cewa Nasir El-Rufai bai sha’awar zama minista a sabuwar gwamnatin tarayya.

Nasir El-Rufai bai sha’awar yin aiki da Bola Ahmed Tinubu bayan abin da ya faru a wajen tantance wadanda ake so su zama ministoci a kasar nan.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Bada Sunan Wanda Zai Canje Shi, Ya Cire Sha’awar Zama Ministan Tinubu

Da aka yi zama da tsohon gwamnan na jihar Kaduna a makon nan, wasu majiyoyi sun shaida cewa ya fadawa Bola Tinubu bai sha’awar rike mukami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.