Rushewar Masallaci: Gwamnonin Arewa Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Masarautar Zazzau

Rushewar Masallaci: Gwamnonin Arewa Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Masarautar Zazzau

  • Gwamnonin arewa sun jajatawa daukacin al'ummar Musulmi kan ibtila'in da ya afkawa masallata a Masallacin fadar zazzau
  • Babban masallacin masarautar Zazzau ya ruguje a ranar Juma'a ana tsaka da sallar la'asar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane
  • Kungiyar gwamnonin arewan ta mika ta'aziyyarta ga masarautar Zazzau, gwamnatin Kaduna, yan uwan mamatan da al'ummar Musulmi baki daya

Kungiyar gwamnonin arewa ta mika ta'aziyya tare da jajanta wa iyalan mutanen da ruftawar masallacin fadar Zazzau ya ritsa da su, wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka shida da jikkata wasu bakwai.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki mai rikita zuciya.

Gwamnonin arewa sun mika ta'aziyya ga Sarkin Zazzau
Rushewar Masallaci: Gwamnonin Arewa Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Masarautar Zazzau Hoto: Leadership
Asali: UGC

Gwamna Yahaya ya bayyana cewa rugujewar masallacin ya tayar da hankalin jama’a ba wai a tsohon birni kadai ba, har ma a fadin kasar baki daya, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Rufin Masallacin Fadar Sarkin Zazzau Ya Ruftawa Mutane Yayin Da Ake Sallah, An Rasa Rayyuka

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tunaninmu da addu'o'i na tare da wadanda wannan ibtila'i mai rikita zuciya ya shafa. A cikin wannan mawuyacin lokaci, muna tare da iyalan wadanda abin ya ritsa da su, muna ba da goyon bayanmu da jajantawa yayin da suke cikin bakin ciki da radadi."

Ya kamata a dauki matakai don hana sake afkuwar lamarin, gwamnonin arewa

Gwamna Yahaya ya jaddada bukatar hukumomin da abin ya shafa su binciki lamarin da ke kewaye da wannan lamari mai cike da bakin ciki sannan su sanya matakan da ya dace don hana sake afkuwar lamarin, rahoton Nigerian Tribune.

Ya ce:

“Ya zama wajibi mu yi koyi darasi daga wannan ibtila'in tare da aiwatar da ingantattun matakan kariya don kare rayuka da kuma kiyaye tsarkin wuraren ibada.
"Ba da kariya da tsaro a cikin wuraren ibada na da matukar muhimmanci, kuma dole ne mu hada kai don tabbatar da lafiyar yan kasarmu yayin da suke gudanar da ayyukan ibada."

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro An Dura Gungun ‘Yan ta’adda Cikin Dare

Shugaban kungiyar ta NSGF ya mika ta'aziyya ga Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, gwamnatin jihar Kaduna da kuma daukacin al'ummar Musulmi gaba daya.

Gwamnan ya roki Allah Madaukakin sarki da ya sakawa mamatan da Aljannat Firdaus sannan ya kuma bai wa iyalan wadanda suka rasu hakuri, ya kuma gaggauta bai wa wadanda suka jikkata lafiya.

Kungiyar CAN ta jajantawa Musulmai kan rushewar masallacin Zazzau

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta jajantawa al’ummar musulmi mazauna garin Zaria a jihar Kaduna da ma daukacin al’ummar kasar dangane da mace-mace da jikkatar masallata da aka samu a yayin da masallaci ya ruguje a Zariya.

Idan baku manta ba, a ranar Juma’a ne aka samu samu aukuwar wani iftila’i a Zaria, inda ginin masallaci ya ruso kan masallata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel