Dubu Ta Cika, an Kama Mutumin da Ya Siyar da Jikarsa a Kan Kudin da Bai Haura N700,000 Ba

Dubu Ta Cika, an Kama Mutumin da Ya Siyar da Jikarsa a Kan Kudin da Bai Haura N700,000 Ba

  • An kama wani mutumin da ya siyar da jikarsa jaririyar da aka haifa a ranar da ta zo duniya, lamarin da ya dauki hankali
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an kamo wanda ya siya tare da wacce ta yi dillacin wannan aika-aika
  • Ana yawan samun matsaloli irin wannan a Najeriya, kuma jami’an tsaro kan tsaya tsayin daka wajen kamo masu laifin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani mutum mai suna Monday Chukwuka da ake zargi da sayar da jikarsa mai kwana daya a duniya a kan kudi naira 700,000.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama mutumin ne a maboyarsa da ke yankin Ibafo a jihar Ogun, bayan wani sahihin rahoton sirri da aka samu, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dama-dama: Davido ya sake sakin sabon bidiyon wakar batanci ga Muslunci a Twitter

Da yake magana yayin da yake gabatar da mutumin a hedikwatar ‘yan sanda, Eleyele, Ibadan, ranar Asabar, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, PPRO, Adewale Osifeso ya bayyana yadda lamarin ya faru.

An kama wanda ya siyar da jikarsa
Kaka ya siyar da jikarsa a Oyo | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Osifeso ya bayyana cewa a bayanan da suka fito daga hirar jami’an leken asiri da mahaifin matar da ta haifi jajiriyar, Mr Monday ya amsa lafinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi bayani dalla-dalla yadda ya dauki jaririyar daga hannun mahaifiyarta (diyarsa mai jego) a lokacin da ta haihu, da sunan zai mika ta ga wanda zai kula da ita.

Daga nan ne ya yi saraf ya siyar da jaririyar a kan kudi N700,000 a wani yankin jihar Abia da ke Kudancin Najeriya.

An gano wacce ta siya jaririyar

Wanda ake zargi da siyan jaririyar mai suna Favor Chukwuka ta ce ta sayi jaririyar ne biyo bayan yadda wasu ma’aurata suka bayyana bukatar a nemo jaririn siyarwa saboda ba sa haihuwa.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Yadda Masu Rike da Madafan Iko Su ka yi wa El-Rufai Taron Dangi

A cewarta, an biya ta kudi N50,000 a matsayin ladan nemo musu inda za su siya jariri da kuma dillancinsa, rahoton Vanguard.

A gefe guda, sauran wadanda rundunar ta kama sun hada da ‘yan fashi da makami, ‘yan daba dauke da muggan makamai, ‘yan baranda da suka kware wajen satar motoci, da mashahuran masu ba ‘yan ta’adda mafaka laifuka da dai sauransu.

An kama wasu sun siyar da jariri

A wani labarin, jami'in hukumar da ke yaki da fataucin bil'adama ta jihar Edo, sun cafke wani mai suna Anthony Igbinogun dan shekaru 48, tare da budurwarsa Joy Umukoro, ‘yar kimanin shekara 28.

An kama saurayin da budurwar tasa ne bisa laifin sayar da jaririnsu dan wata daya domin samun kuɗin shan kwayoyi, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Haka nan kuma, jami'an sun kama waɗanda ake tuhumar tare da wata abokiyarsu mai suna Precious James, yar kimanin shekaru 26, da ta taimaka wajen hadasu da wanda ya sayi jaririn, a Fatakwal ta jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Mace ta yi Karar Saurayi a Kotu, Ya Yaudare ta Bayan ta Kashe Masa N0.9m a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.