Babban Fasto Ya Bayyana Hanya 1 Da Za a Raba Tinubu Da Shugabancin Najeriya
- Manyan ƴan adawa Atiku da Peter Obi na ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa inda su ke fatan samun nasara a kotu
- Akwai ƴan Najeriya da dama da suka yi amanna cewa kotu za ta tsige shugaban ƙasa Bola Tinubu daga kan muƙaminsa
- Fasto Abel Boma ya saki sabon hasashe kan batun taƙaddamar zaɓen na shugaban ƙasa wanda ya goyi bayan Tinubu da APC
Port Harcourt, jihar Rivers- Wani babban fasto mai zama a birnin Port Harcourt, fasto Abel Tamunominabo Boma, ya bayyana cewa idan ƴan Najeriya suka ci gaba da sukar Shugaba Tinubu, shugaban ƙasar zai kammala wa'adinsa na mulki.
Da yake magana a cikin wani bidiyo da aka sanya a shafinsa na Youtube, fasto Boma ya bayyana cewa tabbas idan mafi yawan ƴan Najeriya suka ci gaba da caccakar Shugaba Tinubu, zai yi nasara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
Fasto ya yi magana kan batun tsige Tinubu
Idan ba a manta ba dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), a ranar 1 ga watan Maris ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar zaɓen ta bayyana cewa Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne ya samu ƙuri'u 8,794,726, inda ya lallasa Atiku Abubakar da Peter Obi, waɗanda suka samu ƙuri'u 6,984,520 da 6,101,533 kowanen su.
A cikin ƙararrakin da suka shigar a kotu, Atiku da Peter Obi sun yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen.
Amma fasto Boma ya bayyana cewa abu ne mai matuƙar wahalar gaske a sauke Shugaba Tinubu daga kan mulki.
A kalamansa:
"Babu abinda za ku yi a kotu, zai yi mulki, zai yi nasara."
"Ubangiji ya ce idan kuka ci gaba da nuna masa tsana, zai tsare shi sannan ya kare shi."
Gaskiyar Zance Kan Goyon Bayan Tinubu Da Mary Odili Take Yi
A baya rahoto ya zo kan gaskiyar zance dangane da batun cewa tsohuwar alƙaliyr kotun ƙoli na yi wa Shugaba Tinubu aiki domin ya yi nasara a kotun zaɓe.
Mai shari'ar ta fito fili ta musanta wannan zargin sannan ta yi barazanar maka waɗanda suka yi mata wannan sharrin ƙara a gaban kotu.
Asali: Legit.ng