Sojin Najeriya Sun Bayyana Cewa Shirin Yin Juyin Mulki Ga Tinubu Ba Zai Yi Nasara Ba A Kasar
- Rundunar tsaron Najeriya ta musanta zargin cewa ta na shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu
- Rundunar ta ce ba za ta saurari zugi daga wasu tsiraru marasa kishin kasa ba dake neman a kifar da Tinubu
- Wannan na zuwa ne bayan wasu na hurewa rundunar kunne kan kifar da gwamnatin Najeriya kamar yadda aka yi a Nijar
FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta ce akwai wasu marasa kishin kasa da ke tunzura ta don yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.
Rundunar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta, Birgediya Tukur Gusau a safiyar yau Asabar 12 ga watan Agusta.
Me rundunar ta ce kan kifar da Tinubu?
A cikin sanarwar da ya aikewa Aminiya, Gusau ya bayyana masu kulle-kullen da wasu marasa kishin ci gaban Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kakakin hukumar bai yi karin haske ko ya bayyana wadanda ake zargi da hurewa rundunar kunne ba a kasar, Daily Trust ta tattaro.
A cewarsa:
"Wannan wani shiri ne na kawar da hankulan sojojin wurin yin abin da ya ce kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya daura musu."
Ya ce babu wata zuga da za ta haddasa sojojin yin juyin mulki a Najeriya ganin yadda aka sha wahala kafin samun dawowar dimukradiyya a kasar.
Meye ya jawo martani kan kifar da Tinubu?
Gusau ya ce tsarin dimukradiyya ya na kawo ci gaba don haka duk abin da zai kawo cikas ga tsarin za su yi fatali da shi.
Ya kara da cewa, sojojin za su ci gaba da aikin kare kasar kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulki madadin sauraron wasu gurbatattu daga kasar
Gusau ya ce rundunar karkashin jagorancin babban hafsanta, Christopher Musa ba za su yi karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar ba.
Wannan martani na zuwa ne bayan wasu na zuga sojojin su kwace mulki daga farar hula ganin yadda suka shafe shekaru suna mulki ba tare da kawo karshen matsalolin kasar ba, cewar Channels TV.
Sojin Najeriya Sun Tura Sako Ga 'Yan Ta'adda
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta gargadi 'yan ta'adda da su mika wuya ko kuma su aika su lahira.
Ta ce ba za su zauna teburin sulhu da gurbatattu da suka zama barazana ga zaman lafiyar al'ummar kasar ba.
Asali: Legit.ng