Sanata Ningi Ya Bayyana Abinda Sanatoci Suka Gayawa Tinubu Dangane Da Yaki a Nijar

Sanata Ningi Ya Bayyana Abinda Sanatoci Suka Gayawa Tinubu Dangane Da Yaki a Nijar

  • Sanata Abdul Ningi ya bayyana abin da sanatoci suka gayawa Shugaba Tinubu kan batun afkawa Nijar da yaƙi
  • Sanatan mai wakiltar Bauchi ta tsakiya ya bayyana cewa sanatocin basu aminta da batun yaƙi da Jamhuriyar Nijar ba
  • Ningi ya bayyana cewa kafin a iya tura sojojin ƙasar zuwa fagen daga a wata ƙasa, dole sai majalisun tarayya sun zauna

FCT, Abuja - Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya bayyana cewa majalisar dattawa ta gayawa Shugaba Tinubu cewa ya cire yaƙi a matsayin ɗaya ɗaga cikin hanyoyin dawo da dimokuraɗiyya a Jamhuriyar Nijar.

Sanata Ningi a cikin wani shirin Channels tv mai suna 'Politics Today' a ranar Juma'a, ya bayyana cewa dole sai majalisun tarayya sun zauna kafin a iya tura sojojin ƙasar nan fagen daga ko ina ne a faɗin duniya.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwaddibuwa Ya Ayyana Sojojin Nijar a Matsayin 'Yan Ta'adda, Ya Fadi Abinda Ya Kamata a Yi Mu Su

Sanatoci sun yi fatali da batun yaki da Nijar
Sanatoci sun ce sam ba batun yaki da Nijar Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Ningi ya bayyana cewa shugaban ƙasar yana da damar da zai nemi izni daga wajen sanatocin, amma kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya yi tanadin cewa dole sai majalisun tarayya sun zauna kafin a iya tura sojojin ƙasar nan zuwa fagen daga.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ya aike mana da wasiƙa inda ya yi bayanin abin da ke faruwa a ECOWAS wacce mu ka karanta sannan mu ka gaya masa kai tsaye cewa ba maganar yin yaƙi, a ji da wasu abubuwan daban ba yaƙi ba."

Sanatan ya kuma bayyana cewa sanatocin sun yaba da ƙoƙarin da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) bisa ƙoƙarin da su ke yi domin warware rikicin shugabancin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.

Sanatocin sun yaba wa Tinubu

"Har yaba masa mu ka yi. Mun gaya masa cewa juyin mulki ba abu ne wanda za a tattauna ko amincewa da shi ba. Babu abin da zai sanya a yi juyin mulki." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Gaskiya Ta Fito Kan Makudan Kudaden Da Sanatoci Suka Samu Domin Shakatawa Lokacin Hutu

Sanata Ningi shi ne shugaban ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya, wacce ta yi fatali da yin amfani da ƙarfin soja a Jamhuriyar Nijar.

A cewar sanatan, tarihi da dangantakar dake a tsakanin Najeriya da Nijar daɗaɗɗen abu ne, inda ya bayyana cewa ƙasashen biyu ɗan Juma ne da ɗan Jummai, kawai taswirar da ƴan mulkin mallaka suka yi ce ta raba su.

Shehu Sani Ya Caccaki Tinubu Da ECOWAS

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Ƙaduna ta Tsakiya ya caccaki Shugaba Tinubu da ƙungiyar ECOWAS kann batun amfani da ƙarfin soja a Nijar.

Shehu Sani ya gargaɗe su da su yi taka tsan-tsan kan matakan da su ke shirin ɗauka kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng