Yan Najeriya Da Ke Zaune A Nijar Sun Roki Tinubu Da Ya Kwaso Su Zuwa Gida Saboda Barazanar Hari

Yan Najeriya Da Ke Zaune A Nijar Sun Roki Tinubu Da Ya Kwaso Su Zuwa Gida Saboda Barazanar Hari

  • Yayin da kungiyar ECOWAS ke shirin afkawa Nijar, 'yan Najeriya da ke kasar sun roki Shugaba Tinubu ya kawo musu dauki
  • Sun bayyana cewa 'yan Nijar musamman masu goyon bayan sojojin suna musu barazana
  • Sun roki kungiyar ECOWAS da ta janye wannan kudiri na tura dakaru kasar Nijar don yaki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar - 'Yan Najeriya da ke rayuwa a Jamhuriyar Nijar sun roki gwanatin Tarayya da ta kwaso su a kasar don gudun shiga yamutsin yaki.

Sun bayyana haka ne yayin da kungiyar ECOWAS ke shirin afkawa Nijar don dawo da mulkin dimukradiyya.

'Yan Najeria da ke Nijar sun roki Tinubu ya kwaso su zuwa gida
Yan Kasar Nijar Kenan Da Ke Nuna Goyon Baya Ga Sojojin Juyin Mulki. Hoto: Punch.
Asali: Facebook

Meye 'yan Najeriya a Nijar ke cewa?

Sun bayyana fargabar farmaki daga Nijar ganin yadda Shugaba Tinubu ne ke jagorantar ECOWAS da kuma yadda 'yan kasar ke goyon bayan sojojin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Kungiyar AU Ta Fadi Shirinta Na Taimakon ECOWAS Kan Afkawa Nijar, Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin Nijar da ya gudo zuwa Nijeriya Kafin rufe iyaka, Maina Bukar ya fadawa Punch cewa 'yan kasar na jin haushin 'yan Najeriya saboda rufe iyaka.

Ya ce Nijar ta dogara ne da Najeriya wurin samun kayan masarufi kafin rufe iyakar da Najeriya ta yi, Opinion Nigeria ta tattaro.

Ya ce:

'Yan Nijar na jin haushin mu musamman rufe iyaka da aka yi, saboda yawancin kayan masarufi da suke amfani da shi daga Najeriya suke samu.
"Wani amini na daga Diffa wanda ke goyon bayan sojojin ya fara sauya mini fuska."

Shin 'yan Nijar na goyon bayan sojoji?

Wani mai suna Musa Ali da ya gudo zuwa jihar Borno daga Nijar ya bayyana halin da suke ciki.

Ya ce:

"Mafi yawan 'yan Nijar da ke goyon bayan sojojin juyin mulki na mana barazana a kasar.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

"Suna jin haushin mu saboda rawar da Najeriya ke takawa wurin yakarsu da ECOWAS ke shirin yi, ganin cewa fadan cikin gida ne."

Wani lakcara da ke koyarwa a wata jami'a a Nijar, Yahaya Abdullahi ya ce ya kamata ECOWAS ta duba halin da daliban Najeriya za su shiga.

Ya ce tura dakarun zai kawo matukar cikas ga karatun dalibai musamman daga Najeriya da ke karatu a Nijar.

Kasashen Nahiyar Turai da dama sun kwashe 'yan kasashen su a Nijar don gudun fadawa cikin rikici, CNN ta tattaro.

ECOWAS Ta Shirya Tura Dakaru Kasar Nijar

A wani labarin, Kungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta da su tsaya cikin shiri don afkawa kasar Nijar.

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin ganawa ta karshe da suka yi bayan hambarar da Mohamed Bazoum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.