Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Za Su Dawo Aiki Ranar Asabar
- An buƙaci likitoci masu neman ƙwarewa da su koma bakin aikinsu daga ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, a faɗin ƙasar nan
- Wannan umarnin ya fito ne daga baƙin shugaban ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD), Innocent Orji
- A cikin wata ƴar gajeruwar sanarwa da ya fitar a daren ranar Juma'a, Orji ya sanar da dakatar da yajin aikin da ƙungiyar ke yi
FCT, Abuja - Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da dakatar da yajin aikin da take yi a faɗin ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Innocent Orji, shi ne ya sanar da hakan a daren ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta.
Kamar yadda Channels tv ta rahoto, ya bayyana cewa:
"Barka da yamma. Mun dakatar da yajin aiki. Za mu dawo bakin aiki gobe (Asabar) da misalin ƙarfe 8:00 na safe. Za mu yi duba kan ci gaban da aka samu a cikin sati biyu."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan matakin na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan ƙungiyar ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Buƙatun NARD a wajen gwamnatin tarayya
A cewar shugaban ƙungiyar, likitocin suna neman a biya musu buƙatu takwas ciki har da, ɗaukar sabbin likitoci domin maye gurbin waɗanda suka bar ƙasar nan ko suka rasu.
A kalamansa:
"Mambobin mu suna shan wahala. Ƴan Najeriya na shan wahala. Idan babu likitoci masu yawa a asibiti, hakan barazana ce ga samar da ingantaccen kiwon lafiya. Kuma babu wanda ya fito ya gaya mana cewa abin da mu ke faɗa ba gaskiya ba ne."
"Gwamnati a karan kanta ta kafa kwamiti wanda ya zo da hanyoyin da za a bi tun watan Fabrairun wannan shekarar, meyasa har yanzu ba sanar da su ba?"
Ya zargi gwamnati da kasa biya musu buƙatun su. Shugabannin Ƙungiyar dai sun gana da wasu sanatoci a ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
NARD ta sanar da tsunduma yajin aiki ne a ranar 25 ga watan Yulin 2023, kan buƙatu masu yawa da suka haɗa da ƙarin albashin likitoci.
Sabon Binciken Masana Lafiya
A wani labarin kuma, wani sabon binciken masana a ɓangaren kiwon lafiya ya bayyana adadin takun da mutum yakamata ya riƙa yi a rana domin ƙara tsawancin kwana.
Binciken na masana ya nuna cewa idan ɗan Adam na yin taku 4,000 a rana, hakan zai rage saurin mutuwa.
Asali: Legit.ng