“Ina Biyan Miliyan 1.8 Duk Wata: Matashi Ya Nuna Dan Karamin Gidan Da Yake Haya a Landan, Ciki Ya Hadu

“Ina Biyan Miliyan 1.8 Duk Wata: Matashi Ya Nuna Dan Karamin Gidan Da Yake Haya a Landan, Ciki Ya Hadu

  • Wani matashi da ke zama a UK ya nunawa mutane dan karamin gida da yake biyan £1,850 (N1,805,122.14) duk wata a matsayin kudin haya
  • Yayin da yake zagayawa don nuna yadda gidan mai daki daya yake, ya nunawa mutane inda zai iya hutawa da abokansa da aiki
  • Yan mata da dama da suka kalli bidiyon sun ce za su so sanin ko bai da aure ko yana bukatar abokiyar zama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya da ke zama a UK ya magantu kan yawan kudin da yake biya duk wata a dan karamin wurin da ya karba haya.

Da yake zantawa da wani hazikin dan Najeriya mai daukar bidiyo da ba da labari, Tayo Aina, mutumin ya bayyana cewa kudin hayar gidansa duk wata £1,850 (N1,805,122.14) ne.

Kara karanta wannan

“A Ina Asibitinka Yake?” Kyakkyawan Likita Ya Tashi Kan Yan Mata Yayin da Ya Saki Zafafan Hotunansa a Wajen Aiki, Sun Zauce

Matashi da gidan da yake haya a Landan
“Ina Biyan Miliyan 1.8 Duk Wata: Matashi Ya Nuna Dan Karamin Gidan Da Yake Haya a Landan, Ciki Ya Hadu Hoto: @tayoainafilms
Asali: TikTok

Kudin haya duk wata a UK

Ya zagaya cikin gidan don nuna yadda yake da irin tsarin ciki a wani bidiyon TikTok, yana mai cewa irin wannan ya shahara a UK. A cikin dakin nasa, kwabansa na kallon gadonsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashin wanda yake mazaunin UK ya ce yana son yadda dan karamin gidansa yake matsayin wajen aiki, wurin zama, wajen holewa da zama da abokai.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Gift ta ce:

"Wannan gayen masanin fasaha ne, babu abun da wani zai fada mani."

Jessie.snow101 ta yi ba'a:

"Baka da aure....amma soson da ke cikin bayi mai kalar ruwan hoda."

Ren33 ya ce:

"Yallabai ka gyara lambunka."

Makena wilkinson ya ce:

"Ainahin albashina shine kudin hayarka. Ya Ubangiji."

huxo1 ta ce:

"Na so wannan, gaye mai cike da kwanciyar hankali ba mutane da ke surutu kan 700 a wata ba."

Kara karanta wannan

“Miliyan 4 Aka Biya Ni”: Matashi Da Ya Rikide Ya Koma Mace Ya Yi Tafiyar Rangwada Da Takalma Masu Tsini, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Hana Manzali ta ce:

"Nawa yake samu albashi. Ina gwagwarmayar biyan 350£ na dakina a Faransa a matsayin daliba."

De-Elites Business Magazine ya ce:

"Kimanin naira miliyan 1.9 kenan duk wata, Toh, na kula."

Dan NYSC ya mayar da kudin da aka tura masa bisa kuskure

A wani labari na daban, wani mai yi wa kasa hidima, Adekunle Isaiah Oluwaseun, ya samu shigar naira miliyan 20 a asusun bakinsa a kawanan nan wanda aka tura masa bisa kuskure kuma ya dauki mataki da mutane da dama suka bayyana a matsayin gaskiya.

Matashin wanda ya kammala karatunsa daga jami'ar Lagas ya ce ya kadu sannan ya firgita da ya ga alat din, yana mai cewa N1,521 ne kacal da shi a asusun bankinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng