Gwamnati Ta Dakatar Da Basaraken Gargajiya Saboda Rashin Biyayya A Jihar Ekiti

Gwamnati Ta Dakatar Da Basaraken Gargajiya Saboda Rashin Biyayya A Jihar Ekiti

  • Gwamnatin jihar Ekiti ta dakatar da wani mai sarautar gargajiya a jihar bayan zarginsa da karfa-karfa da wuce gona da iri da rashin biyayya
  • Wanda aka dakatar din Cif Gabriel Botunde shi ne mai sarautar gargajiya na Imesi Ekiti a karamar hukumar Gbonyi ya ki amsa gayyatar gwamnati
  • Mataimakiyar gwamnan jihar, Cif Monisade Afuye ita ta bayyana haka yayin jagorantar zaman a ofishinta a jiya Alhamis 1 ga watan Agusta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ekiti – Gwamnatin jihar Ekiti ta dakatar da wani mai sarautar gargajiya, Cif Gabriel Bodunde a Imesi Ekiti da ke karamar hukumar Gbonyin a jihar.

An dakatar da mai sarautar bisa zargin karfa-karfa da rashin mutunta na gaba da kuma makarkashiya ga Oba Oltunji Olatunde, sarkin yankin da ke gaba da shi a matsayi.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar Sun Aikawar Da Wata Sabuwar Doka A Kasar, Janar Tchiani Ya Yi Bayani

Ekiti ta dakatar da basarake saboda rashin biyayya ga gwamnati
Gwamnatin Jihar Ekiti Ta Dauki Matakin Ne Don Ladabtar Da Basaraken. Hoto: Radio Nigeria.
Asali: Facebook

Me ake zargin basaraken da aikatawa?

Ana kuma zarginshi da tayar da hankula ta hanyar kama mutane ba bisa ka’ida ba da ke kawo tashin hankula a yankin, cewar New Telegraph.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakiyar gwamnan jihar, Cif Monisade Afuye ita bayyana haka yayin karbar korafin a ofishinta a jiya Alhamis 10 ga watan Agusta.

Daily Trust ta tattaro cewa Cif Bodunde bai samu halartar zaman ba kuma bai tura kowa don wakiltarsa a ganawar ba.

Wane hukunci aka yanke masa?

Oba Olatunde tun farko ya bayyana rashin jin dadinsa ganin irin kokarin da suka yi don neman maslaha da Cif Bodunde amma ya ki, Tribune ta tattaro.

Ya ce kin amsa gayyatar gwamnatin jihar wannan ya nuna tsantsan girman kansa da kuma rashin mutunta hukuma inda ya ce hakan babban laifi ne na musamman.

Kara karanta wannan

Orire Agbaje: Bayanin ‘Yar Jami’ar da ta Shiga Muhimmin Kwamitin da Tinubu ya kafa

Cif Monisade ta yanke hukuncin dakatar da shi har sai an kammala bincike a kansa.

Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya A Legas

A wani labarin, wani babban basarake mai suna Oba Azeez Dada Aluko ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.

Marigayin shi ne mai sarautar yankin Idimu da ke Egbe Idimu a jihar Lagos wanda ya rasu a ranar 14 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Egbe Idimu, Sanyaolu Olowoopejo ya fitar inda ya bayyana mutuwar basaraken da babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.