Kotu Za Ta Saurari Karar Emefiele Da Gwamnatin Tarayya a Ranar 15 Ga Watan Agusta
- Wata babbar kotun tarayya a jihar Legas ta sanya ranar da za ta saurari ƙarar da aka shigar kan ci gaba da tsare Godwin Emefiele
- Alƙalin kotun ya sanya ranar 15 ga watan Agusta a matsayin ranar sauraron ƙararrakin da gwamnatin tarayya da Emefiele suka shigar a gabanta
- A baya dai kotu ta bayar da belin dakataccen gwamnan babban bankin na Najeriya kan kuɗi har N20m
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Legas - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a jihar Legas, a ranar Alhamis ta sanya ranar 15 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta saurarin ƙara kan tsare Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya.
Emefiele yana fuskantar tuhumomi guda biyu kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba, cewar rahoton The Punch.
A lokacin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan masu shigar da ƙara, K.A. Fagbemi, ya buƙaci kotun da ta saurari ƙarar gwamnatin tarayya kan batun belin Emefiele.
Kotu Ta Tsare Fitaccen Malamin Addini Kan Zargin Mallakar Bindiga AK-47 A Coci, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
Fagbemi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta fara shigar da ƙarar ta sannan ta aike wa da lauyoyin wanda ake ƙara a ranar 4 ga watan Agusta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake mayar da na sa martanin, lauyan Emefiele, Victor Opara, ya bayyana cewa bai kamata a ba gwamnatin tarayya fifiko kan lokacin da ta shigar da ƙarar ba saboda an yi biris da umarnin kotun kan bayar da belin.
Opara ya nemi kotun da saurari ƙararrakin ɓangarorin biyu a rana ɗaya, rahoton Channels tv ya tabbatar
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da wani abin da za ta yi fargaba akai saboda wanda ake ƙarar yana tsare a hannunta.
Wacce matsaya kotun ta cimma?
Bayan ya gama sauraron bayanan ɓangarorin biyu, alƙalin kotun ya yanke hukuncin cewa kotun za ta saurari ƙararrakin ɓangarorin biyu a ranar 15 ga watan Agusta.
Idan ba a manta ba dai a ranar 25 ga watan Yuli, mai shari'a Oweibo ya bayar da belin Emefiele kan kuɗi N20m.
Sai dai, alƙalin ya bayar da umarnin cewa a ci gaba da tsare dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya a hannun hukumar gidajen yari ta Najeriya, har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan belinsa.
Jami'an DSS Sun Yi Caraf Da Emefiele
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun sake yin caraf da Godwin Emefiele.
Jami'an na DSS sun dai sake cafke Emefiele ne bayan kotu ta bayar da belinsa kan tuhumar da ake yi masa.
Asali: Legit.ng