Rikicin Nijar: Falana Ya Ce Kwasar Albarkatun Kasa Ne Ke Haifar Da Juyin Mulki a Yammacin Afrika

Rikicin Nijar: Falana Ya Ce Kwasar Albarkatun Kasa Ne Ke Haifar Da Juyin Mulki a Yammacin Afrika

  • Babban lauya ɗan rajin kare haƙƙin bil'adama Femi Falana, ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin Nijar
  • Ya ce ɗibar ma'adinan ƙasashen Afrika da Turawa ke yi ne ya ta'azzara juyin mulkin da ake samu a nahiyar
  • Ya shawarci shugabannin Afrika da su yi tsare-tsaren da kowace ƙasa za ta riƙa amfana da arziƙinta yadda ya dace

Babban lauyan nan kuma dan rajin kare haƙƙin bil'adama, Femi Falana SAN, ya yi magana dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar.

Ya ce kwashe albarkatun ƙasa da Turawan mulkin mallaka ke yi ne ya ƙara janyo yawaitar samun juyin mulki a ƙasashen Afrika ta Yamma.

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Femi Falana ya shawarci shugabannin ECOWAS
Femi Falana ya bayyana abubuwan da ke janyo yawaitar juyin mulki a Afrika. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Kungiyar CAN Ta Faɗawa Tinubu Ainihin Matakin Da Ya Kamata Ya Ɗauka

Kwasar albarkatun na daƙile arziƙin wasu ƙasashen na Afrika

Falana ya ce yawaitar juyin mulkin da ake samu, yana da alaƙa mai ƙarfi da rashin samar da tsarin tafiyar da tattalin arziƙin ƙasashen yadda ya dace.

Ya ce katsalandan ɗin da ƙasashen da suka yi wa Afrika mulkin mallaka ke yi na ƙara taimakawa wajen ruguza tattalin arziƙin ƙasashen na Afrika da ke tasowa.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan abubuwan ne ke taruwa su yi yawa, daga nan sai ka ga 'yan ƙasa suna nuna goyon bayansu a duk lokacin da aka samu juyin mulki.

Ƙarin wasu abubuwan da ke janyo juyin mulki

Lauyan ya ƙara da cewa ƙarin wani abinda ke janyo juyin mulki a Afrika ta Yamma shi ne, tsare-tsaren da hukumomin ƙasashen wajen ke zuwa da su ga ƙasashen na Afrika.

Ya ce tsaruka masu tsauri a kan talakawa da hukumomin ƙasashen waje irin su bankin duniya, da kuma hukumar ba da lamuni ta duniya (IMF) ke zuwa da su na da matuƙar tasiri wajen ƙara tunzura jama'a.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Kasashen Afrika 10 Da 'Yan Ƙasarsu Suka Fi Na Kowace Arziƙi a 2023

Ya ce irin hakan ne ke sanya 'yan ƙasashen na Afrika goyon bayan sojoji a duk lokacin da aka samu juyin mulki a ɗaya daga cikinsu kamar yadda Channels ta wallafa.

Ya shawarci shugabannin na ECOWAS da su yi ƙoƙarin kawo ƙarshen kwashe arziƙin ƙasashensu da ake yi, ta yanda 'yan ƙasa za su samu damar juya arziƙin na su da kansu.

Kungiyar CAN ta faɗi illar amfani da ƙarfin soji kan Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan maganar da kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN ta yi, na nuna goyon bayanta ga ɗaukar matakai na diflomasiyya a kan jamhuriyar Nijar.

Kungiyar ba ta goyi bayan ɗaukar matakai na soji ba, inda ta ce hakan zai iya janyo gaba tsakanin Najeriya da maƙwabtanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng