Kisan Malamin Addinin Musulunci Ibrahim Albani: 'Yan Sanda Sun Saka Dokar Hana Fita a Gombe

Kisan Malamin Addinin Musulunci Ibrahim Albani: 'Yan Sanda Sun Saka Dokar Hana Fita a Gombe

  • Rundunar 'yan sandan jihar Gombe, ta sanar da dokar taƙaita zirga-zirga a faɗin jihar
  • Hakan ya biyo bayan kisan gillar da wasu da ake tunanin 'yan fashi ne suka yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci
  • Kakakin rundunar 'yan sandan na jihar Gombe, Mahid Abubakar ne ya sanar da hakan ga manema labarai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gombe - Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun kashe wani malamin addinin Musulunci Sheikh Ibrahim Albani, a gidansa da ke Gobona, a rukunin gidaje na Tabra da ke garin Gombe.

Biyo bayan hakan ne rundunar 'yan sandan jihar, ta sanar da sanya dokar taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 12 na dare zuwa 6 na safe a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar, shi ne ya tabbatarwa da jaridar TheCable hakan a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Mai Laifi Ya Gantsarawa Ɗan Sanda Cizo a Yatsa Lokacin Da Za a Kama Shi

An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a Gombe
'Yan sanda sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga a Gombe. Hoto: The Punch
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan fashi ne suka kashe Sheikh Ibrahim Albani

Kakakin 'yan sandan ya ce mummunan lamarin ya faru ne gab da asubahin ranar Laraba, da misalin ƙarfe 3 na dare.

Ya ce wasu 'yan fashi ne su hudu, waɗanda suka rufe fuskokinsu da ƙyalle, suka haura gidan malamin da tsakar dare, sannan suka buƙaci ya ba su kuɗi.

Sai dai malamin ya ƙi amincewa da hakan, inda ya shaida musu cewa ba ya da kuɗin da zai ba su kamar yadda matarsa ta faɗawa jami'an tsaro.

Dalilin da ya sa suka kashe malamin

Mahid Abubakar ya bayyana cewa, malamin ya yi ƙoƙarin yakice ƙyallen da ke fuskar ɗaya daga cikin 'yan fashin domin gane ko su wanene.

Sai dai hakan bai yi musu daɗi ba, inda suka yi amfani da ɗaya daga cikin wuƙaƙen da suka zo da su wajen halaka fitaccen malamin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutane 17

Ya ƙara da cewa tuni kwamishinan 'yan sandan jihar Oqua Etim, ya ba da umarnin tsananta bincike don kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin domin a hukuntasu.

Ya shawarci mutanen jihar da su bai wa jami'an tsaro haɗin kai dangane da dokar ta taƙaita zirga-zirga da aka sanya kamar yadda The Punch ta wallafa.

Barayi sun kone shaguna 20 bayan tafka sata a Gombe

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan mummunar ta'asar da wasu da ake kyautata zaton cewa ɓarayi ne suka yi a tsohuwar kasuwar Gombe.

Barayin sun tafka sata sannan kuma suka kunna wutar da ta cinye shaguna aƙalla guda 20.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng