Yan Bindiga Sun Sace Mutum 14 a Wasu Kauyukan Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Sace Mutum 14 a Wasu Kauyukan Jihar Katsina

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a wasu ƙauyuka gudu uku an ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina
  • Ƴan bindigan waɗanda suka kai farmaki a ƙauyukan cikin tsakar dare, sun yi awon gaba da bayin Allah 14 da basu ji ba basu gani ba
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda ta bayyana cewa ta aike da jami'anta domin tabbatar da an ceto mutanen da cafke ƴan binidigan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da aƙalla mutum 14 a wasu ƙauyuka guda uku na ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Jaridar Channels tv ta rahoto cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutanen ne bayan sun farmaki ƙauyukan su da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya, Sun Tura Masu Yawa Zuwa Barzahu

Yan bindiga sun kai hari a jihar Zamfara
Yan bindigan sun farmaki ƙauyukan ne cikin dare Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Ƙauyukan sun haɗa da Yakkaka a gudndumar Gazari, Yallagwada a gundumar Maibakko da Maiturmi a gundumar Rafin-Iwa.

Ƴan bindigan sun sace mutum bakwai a ƙauyen Yakkaka, mutum shida a ƙauyen Yallagwada da wata mace ɗaya a ƙauyen Maiturmi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, ƴan sakai dake aiki a yankin sun samu nasarar ceto matar da aka sace a ƙauyen Maiturmi.

Haka kuma ƴan bindigan sun kai irin wannan harin a ƙaramar hukumar Dandume mai maƙwabtaka da Sabuwa, inda suka halaka mutum ɗaya a ƙauyen Tudun Ali. Wanda aka halaka ɗin ɗa ne a wajen mai garin ƙauyen.

Menene abinda ƴan sanda suka ce?

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba.

ASP Abubakar ya bayyana cewa tuni ƴan sanda suka bazama neman ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan da kuma cafke ƴan ta'addan.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Hallaka Manomi, Sun Sace Mata 5 Da Maza 2 a Kaduna

Manomi Ya Halaka Dan Bindigan Da Ya Halaka Masa 'Ya'Ya

A wani labarin kuma wani manomi ya nuna halin jarumta inda ya tunkari ɗan bindigan da ya halaka masa ƴaƴa har guda uku a jihar Kaduna.

Manomin dai ya salwantar da rayuwar ɗan ta'adɗan ne bayan sun dawo domim tafiya da shi a cikin gonarsa. Manomin ya cakumi ɗan ta'addan da kokawa inda daga nan ya samu sa'ar aika shi barzahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng