"Dole Ka Yi Murabus": Timi Frank Ya Caccaki Akpabio Kan Batun Kudaden Shakatawar Sanatoci
- Katoɓarar da aka ritsa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio na yi ta rabon kuɗi ga sanatoci, ta tunzura ƴan Najeriya
- Kwamared Timi Frank wani ɗan gwagwarmaya ya bayyana abin da shugaban majalisar ya yi a matsayin izgili ga ƴan Najeriya
- Frank ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya gaggauta raba Akpabio da shugabancin majalisar ta hanyar tilasta shi yin murabus daga muƙaminsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ɗan rajin gwagwarmaya mai kare dimokuraɗiyya, Kwamared Timi Frank, ya caccaki shugaban majalisar dattawa kan bayyana cewa an gwangwaje sanatoci da kuɗaɗe domin su sha shagali a hutun da za su tafi.
Da yake magana a cikin wani bidiyo da ya aike wa jaridar Leadership ranar Laraba da safe, Frank ya bayyana katoɓarar da Akpabio ya yi a matsayin abun kunya da kuma mayar da dimokuraɗiyya da ƴan Najeriya abun tsokana.
Bidiyon Akpabio Yana Sanar Da Cewa An Tura Wa Yan Majalisa Kudaden Shakatawa Yayin Hutu Ya Janyo Cece-Kuce
Frank ya yi kiran da shugaban majalisar dattawan ya gaggauta yin murabus daga muƙaminsa ba tare da ɓata lokaci ba.
Ya bayyana cewa bai dace ba sanatocin su yi watanda da dukiyar ƙasa da sunan hutu a lokacin da ƴan Najeriya ke cikin halin matsin tattalin arziƙi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Frank, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya gaggauta kawo ƙarshen shugabancin Akpabio da abun kunyar da majalisar ke yi ta hanyar gaya masa ya yi murabus ba tare da ɓata lokaci.
Akpabio ya kunyata ƴan Najeriya
Timi ya bayyana abinda Akpabio ya yi abun kunya ne ta hanyar fitowa ya bayyana cewa magatakardan majalisar ya tura wa kowane sanata kuɗi a asusu.
A kalamansa:
"Wannan shine babban izgilin da mu ka gani a cikin ƴan kwanakin nan. Hakan ya sanya na ke faɗi da babbar murya cewa dole Sanata Akpabio ya yi murabus daga shugabancin majalisar dattawa. Ba zai yiwu ya ci gaba da yi wa dimokuraɗiyyar mu da ƴan Najeriya izgili ba."
"Wannan shi ne wanda ya yi wa talakawa izgili a majalisa ta hanyar cewa a bar talakawa su numfasa. Yayin da yake dariya saboda ya san cewa ba za su taɓa bari talakawa su numfasa ba, za su ci gaba da muzguna musu kamar yadda ya nuna ta hanyar raba kuɗaɗen talakawa zuwa aljihunan su."
"Ƴan Najeriya sun sha wahala. Ba mu zaɓi sanatocin mu ba ne domin su zo su kwashe kuɗin talakawa su tafi hutu da su."
Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Ali Pate
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yaba da ƙwazon da Ali Pate ya nuna a lokacin tantance shi domin zama minista a majalisar dattawa.
Shugaban ƙasar ya nuna cewa tsohon ministan ya yi ƙwazo sosai lokacin da ya bayyana a gaban majalisar.
Asali: Legit.ng