Shugaba Tinubu Ya Bayyana Ministan Da Ya Yaba Da Kwazonsa Wajen Tantancewa a Majalisa
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yaba da kwazon da Farfesa Ali Pate ya yi lokacin da ake tantance shi a matsayin minista a majalisar dattawa
- Farfesa Pate yana daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu ya miƙa zuwa ga majalisa domin tantancewa da amincewa da su
- Shugaban ƙasar ya yi wannan yabon ne lokacin da Pate ya raka Darekta Janar ta WTO, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, zuwa fadarsa a ranar Talata
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yaba wa Farfesa Ali Pate, ɗaya daga cikin ministocin da majalisr dattawa ta amince da su, bisa kwazon da ya nuna a lokacin da ake tantance shi a majalisa.
Pate ya taɓa riƙe muƙamin ƙaramin ministan lafiya a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.
Wanene Farfesa Ali Pate?
Kafin a naɗa shi ya zama minista, Pate ya yi murabus daga shugabancin kamfanin 'GAVI- Global Alliance for Vaccines and Immunization' inda ya yi nuni da cewa zai samu muƙami a gwamnatin Shugaba Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Talata, 8 ga watan Agusta, Pate ya raka Ngozi Okonjo-Iweala, Darekta Janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya domin ziyartar Shugaba Tinubu a fadar shugaban ƙasa.
A yayin da suke gaisawa, Shugaba Tinubu ya yaba wa Farfesan bisa kwazon da ya nuna lokacin da ake tantance shi domin zama minista a majalisar dattawa.
Pate, Okonjo-Iweala sun yi aiki a gwamnatin Jonathan
Shugaba Tinubu ya gaya masa cewa ya kalli yadda tantancewar ta sa ta kasance a talbijin.
"Na kalle ka a TV. Ka yi ƙwazo sosai." A cewarsa.
Idan ba a manta ba dai Pate da Okonjo-Iweala sun yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Goodluck Jonathan. Ngozi ta riƙe muƙamin ministan kuɗi da ministan kula da tattalin arziƙi.
Okonjo-Iweala Ta Ziyarci Tinubu
A wani labarin kuma, Darekta Janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO), Dr Ngozi Okonjo-Iweala ta ziyarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Villa.
Okonjo-Iweala ta sanya labule da shugaban ƙasar ne domin tattauna muhimman batutuwa wajen kawo ci gaba ga al'ummar Najeriya a halin matsin da ake ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng