Manyan Abubuwa 12 Da Suka Faru Tun Lokacin Da Aka Yi Juyin Mulkin Nijar
Niamey, Nijar - A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli ne jami'an sojin da ke tsaron fadar shugaban Nijar Muhammed Bazoum, suka kifar da gwamnatinsa.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abdourahmane Tchiani, shugaban dakarun da ke bai wa Bazoum kariya ne ya jagoranci kifar da gwamnatin ta Bazoum.
Hakan ya janyo Allah wadai daga ƙungiyoyi da dama daga sassa daban-daban na duniya.
Daga cikin waɗanda suka nuna adawa da juyin mulkin akwai ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), wacce ta nemi sojojin na Nijar su mayarwa da Bazoum kujerarsa ba tare da ɓata lokaci ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abubuwa 12 da suka faru daga juyin mulkin na Nijar zuwa yau
Legit.ng ta zaƙulo muhimman abubuwa 12 da suka faru daga lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula ta Nijar zuwa yanzu kamar yadda Daily Trust ta tattara.
1. Wa'adin ECOWAS
A ranar Lahadi, 30 ga watan Yuli, shugaban ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa sojojin na Nijar wa'adin kwana bakwai su mayar da mulki.
Sai dai sojojin sun yi burus da wa'adin da aka ba su duk kuwa da barazanar ɗaukar mataki na soji.
2. Rufe iyakoki da katse wuta
Mataki na gaba da Najeriya ta ɗauka shi ne katse wutar lantarkin da take bai wa jamhuriyar ta Nijar.
Haka nan Najeriya ta rufe duka iyakokinta daga shigar da kaya ko fito da su daga Nijar kamar yadda Premium Times ta wallafa.
3. Samun goyon bayan Mali da Burkina Faso
Biyo bayan iƙirarin amfani da ƙarfin sojin da ECOWAS ta yi, ƙasashen Mali da Burkina Faso sun sha alwashin kai wa Nijar ɗauki da zarar an kai ma ta harin.
4. Kwashe 'yan ƙasashen waje
A yayin da abubuwa ke ƙara ɗaukar zafi, manyan ƙasashe irinsu Faransa, Germany da Portugal, sun yi ruguguwar kwashe 'yan ƙasarsu daga Nijar saboda fargabar kada yaƙi ya rutsa da su.
5. Amurka ta goyi bayan Tinubu
Ƙasar Amurka ta jinjinawa Shugaba Tinubu bisa matakin da ya ɗauka a matsayinsa na shugaban ECOWAS, inda ta yi alƙawarin ba kawo agaji a duk sanda ake buƙata kamar yadda aka buga a shafin France 24.
6. ECOWAS ta tura wakilci zuwa Nijar
A cikin ƙoƙarin ganin sojoji sun mayar da mulki hannun fararen hula, kungiyar ECOWAS ta tura tawagar sulhu zuwa jamhuriyar Nijar.
Tawagar ta haɗa da Sarkin Musulmi da kuma tsohon shugaban Najeriya Abdulsalami Abubakar, da kuma Omar Alieu Touray.
7. Nuna goyon bayan sojoji
Da dama daga 'yan jamhuriyar ta Nijar, sun cika Niamey wato babban birnin ƙasar, inda suka nuna goyon bayansu ga sojojin da suka gudanar da juyin mulkin.
8. Dakatar da bayar da tallafi
Biyo bayan juyin mulkin, ƙasar Faransa da Germany ta sanar da dakatar da bayar da tallafi ga jamhuriyar ta Nijar.
9. Sojojin ECOWAS sun buƙaci a bi matakai na diflomasiyya
Biyo bayan taron da shugabannin tsaron ƙasashen ECOWAS suka gudanar, wanda ya samu halartar ƙasashe 10 daga cikin 15, sun zaɓi bin matakai na diflomasiyya wajen warware rikicin na Nijar.
10. Majalisar Dattawa ta yi fatali da buƙatar Tinubu
A ranar Asabar da ta gabata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cewa ba ta amince da tura dakarun soji jamhuriyar Nijar ba kamar yadda ECOWAS ta buƙata.
11. Kulle sararin samaniyar Nijar
A ranar Litinin, 7 ga watan Agusta ne sojojin na Nijar suka sanar da kulle sararin samaniyar jamhuriyar Nijar saboda gudun kar a kawo musu hari ta sama kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
12. Nadin Firaminista
Da yammacin ranar Litinin ne sojojin na jamhuriyar Nijar suka sanar da naɗin Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin Firaministan ƙasar.
Shugabannin addinai su gargaɗi Tinubu kan amfani da ƙarfin soji a Nijar
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan ƙin amincewa da ƙungiyar jama'atu Nasril Islam ta yi kan shirin da Shugaba Bola Tinubu ke yi na amfani da ƙarfin soji wajen dawo da dimokuraɗiyya a Nijar.
Haka nan ƙungiyar limaman majami'o'i, sun buƙaci Tinubu ya dakatar da shirin da ECOWAS take yi na tura sojoji jamhuriyar Nijar.
Asali: Legit.ng